| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya - Hukumomi
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ya ce alƙaluman sun nuna mummunan tasirin da matsalar ta'addanci ta tsawo lokaci ta yi ga yara, musamman kan lafiyar ƙwaƙwalwarsu da iliminsu da kuma makomarsu a gaba.
An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya - Hukumomi
An lalata makarantu fiye da 1000 an kashe malamai da dama a Arewa maso Gabashin Nijeriya

Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa an lalata makarantu fiye da 1,400 a faɗin yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, yayin da aka kashe malamai 2,295, sannan aka raba mutane 19,000 da gidajensu a tsawon shekarun da aka kwashe ana fama da matsalar ta'addanci da rikici a yankin.

Gwamnatin ta kuma ce kimanin yara miliyan uku ne ke buƙkatar tallafin gaggawa na ilimi.

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Gwamna Babagana Umara Zulum a wani Taron Tattaunawa na Ƙasa na Kwanaki biyu da aka kan illar Rikici ga Lafiyar Ƙwaƙwalwar Yara a Nijeriya da aka gudanar a Maiduguri.

Kadafur ya ce alƙaluman sun nuna mummunan tasirin da rikicin na tsawo lokaci ya yi ga yara, musamman kan lafiyar ƙwaƙwalwarsu da iliminsu da kuma makomarsu a gaba.

Ya ce sakamakon tashe-tashen hankulan da aka yi ta fuskanta har bayan samun galaba kan ‘yanta’adda, illar ta kan shafi halayyar yaran da kuma yanayin yarda da amincewarsu da al’ummominsu.

"Yanayin damuwa da tsoro ba sa ƙarewa ko bayan an dikile hare-hare. Ya kan shiga ya zauna a cikin ƙwawƙalwarsu da ke bunƙasa. Sai ya sauya yanayin fahimta da ɗabi'u da kuma yardarsu," in ji shi.

Mataimakin gwamnan ya yi gargaɗin cewa raunin da ba a yi masa magani ba zai iya haifar da ɗacin rai da kangarewa da kuma rauni da kan kai ga ɗaukarsu aiki a ƙungiyoyin ‘yanta’adda.

Ya ce, ayyuka da shiga tsakani na sojoji kaɗai ba za su iya magance sakamakon tsawon lokacin da aka kwashe na ta’addanci ba, yana mai jaddada buƙatar ƙara shirin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da tallafin zamantakewa a ƙoƙarin samar da yanayin nutsuwa da tsaro.

Kadafur ya yi kira da a samar da tsarin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa na ƙasa ga yaran da suka taba fuskantar rikici da ƙara tura ƙwararrun likitocin lafiyar ƙwaƙwalwa zuwa al'ummomin da abin ya shafa, da kuma saka hannun jari mai yawa a fannin ilimi da ayyukan da suka shafi al'umma.

Wakiliyar Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa, Nuhu Ribadu, Daraktan Harkokin Lafiya ta Hukumar Leken Asiri ta Nijeriya, Dr Patience Omokri, ta ce ya kamata a ɗauki mummunan yanayin da yara suka fuskanta a matsayin batun damuwa ga tsaron ƙasa.

Ta ce yaran da suka taɓa fuskantar yanayin rashin tsaro da ayyukan ta'addanci, suna fama da ƙuncin rasa iyaye da gidajensu, sannan wasu an yi garkuwa da su, kana wasu sun fuskanci sauran nau'ikan cin zarafi.

"Yaron da ya taɓa fuskantar tashe-tashen hankula ba wai kawai wanda aka zalunta ba ne. Idan aka bar shi babu taimako, zai iya zama wani a cikin al’umma da ka iya janyo rashin kwanciyar hankali," in ji sakon Ribadu.

Wakilin UNICEF, Francis Otuochi, ya ce yara 270,864 a Borno da Adamawa da kuma Yobe suna buƙatar kulawar lafiyar ƙwaƙwalwa da ta zamantakewa a ƙarƙashin shirin Majalisar Dinkin Duniya na ɗaukar matakai da buƙatun jin’kai na shekarar 2026.

Ya yi kira ga gwamnatoci da su sanya shirin lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin tsarin shirye-shiryen kare yara da kiwon lafiya da ilimi da kuma walwalar jama'a.