Wani dan siyasa kuma mai fafutuka Patrick Lozes ya ce ba a yi wa bakaken fata karin girma a wuraren aiki Hoto: Taskar AP

Mutum tara cikin baƙaƙen fata10 a Faransa sun bayar da rahoton cewa ana nuna musu wariya, matsalar da gwamnatin kasar ta yi wasti da shi, in ji wani dan siyasa kuma mai fafutuka a Faransa Patrick Lozes.

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yi a ranar Litinin da Lozes, shugaba kuma wanda ya kafa kungiya Majalisar Wakilai ta Bakar Fata (CRAN), ya bayyana irin ƙuncin ƙyama da nuna wariyar launin fata da baƙin mutum ke fuskanta a Faransa a ko da yaushe.

Lozes ya jawo hankali ga binciken da wani kamfani mai zaman kansa Ipsos ya gudanar kan bakaken fata a Faransa, yana mai cewa: “bayanan wadanda suka gudanar da binciken ya yi nuni kan yadda ake nuna wariya a fannoni da dama a Faransa.''

''Adadin bakaken fata a Faransa kusan kaso 91 cikin 100, sun ce ana nuna musu wariya a harkokin rayuwarsu na yau da kullum,” in ji Lozes, yana mai cewa hakan na nufin wariyar launin fata ta zama wata babbar matsala ga kusan kowane baƙin Bafaranshe da ke kasar.

Ya bayyana cewa baƙin mutum na fuskantar wariya a wuraren neman gida da aiki a ƙasar.

Lozes ya bayyana cewa: “Idan ka kira ta wayar tarho, ka ce kana son gida, kuma wanda kake magana da shi ya ce akwai gida, da zarar ya gane cewa kai baƙar fata ne, nan take zai iya ce maka ba zai ba ka hayar gidan ba.

"Sannan ba za a ƙara maka wani girma a wajen aiki ba, kuma idan ka nemi aiki da zarar ka tura takardarka bayan wani dan lokaci za a sanar da kai cewa an cike gurbin, amma matsayin a bude yake ga wani da ya nema bayan kai, " in ji Lozes.

Dan fafutukar ya yi nuni da cewa babu wakilcin bakaken fata a Majalisar Dokokin Faransa da sauran manyan matsayi na aikin soji ko kuma masu riƙe da muƙamai a kamfanoni da dai sauransu, Lozes ya ce ana matukar ware bakin mutum a harkokin ci gaba da dama.

Ya bayyana cewa farin mutum na ganin baƙin mutum a matsayin mara "hazaka da basira.”

"Idan aka zabe ka a Majalisar Dokokin kasar, hatta takwarorinka na majalisar za su ringa nuna muka wariya," in ji shi.

Nuna kabilanci daga ƴan sanda

Lozes ya bayyana cewa ƴan sanda a Faransa na yawan nuna ƙabilanci ga baƙaƙen fata, "Idan ka tambayi wani baƙar fata kan ire-iren abubuwan da ke faruwa a rayuwar yau da kullum, yawanci za ka ji ya ce maka ''yawan tambayoyi da bincike da ƴan sanda ke yi wa baƙaƙen fata fiye farin mutum."

Ko da yake ya bayyana cewa ba duka aka taru aka zama daya daga cikin jami'an yan' sandan ba amma '' akwai wariyar launin fata a tsakanin jami'an.''

Ya kuma bayyana cewa ba daidai ba ne a hukunta bakaken fata saboda launin fatar jikinsu, “bai dace ba ana nuna mana wariya a ƙasarmu saboda launin fatarmu.

"Yin haka ba adalci ba ne ga kasa kamar wannan domin ina so ana ganin Faransa a matsayin kasar da ke da adalci kuma wacce ke da daidaito a tsarinta, tare da kawar da duk wani nau'i na wariyar launin fata."

'Bakar fata da kafofin watsa labarai na Faransa'

Lozes ya yi kwatance da irin bangarancin da kafofin watsa labarai ke nunawa game da bakar fata, yana mai cewa: “Ban san dalilan da su sa kafafen watsa labarai ba su cika yada labarin wani laifin da aka aikata a wani wuri ba, sai dai rahotonni kan laifin da wani bakin fata ya aikata tare da jaddada batun.''

Ya kuma bayyana cewa a yanzu kafafen watsa labaran Faransa ba su faye mayar da hankali kan batun wariyar launin fata fiye da yadda ake yi a da ba.

“Yan jarida kalilan ne bakake a mayan kafafe kamar Le Monde ko wata kafar talabijin, shi ya sa nake gaya wa kafafen watsa labarai cewa yana da kyau a rika yada labaran wariyar launin fata, amma sai ka kalli kanka ka yi abin da kake son wasu mutane su yi," in ji shi.

TRT World