An fara jefa kuri'a a ranar Larabar nan a yankin Kashmir da ke karkashin India a zaben 'yan majalisar dokoki mai muhimmanci, wanda shi ne na farko tun 2014.
Za a gudanar da zaben a matakai uku - 18 ga Satumba, 25 ga Satumba da 1 ga Oktoba, sannan a kirga ƙuri'u da sanar da sakamako a ranar 8 ga Oktoba.
"Na jefa kuri'ata don samun cigaba. A shekaru goman da suka wuce, ba mu iya samun hakkin jefa kuri'a ba, ina farin ciki cewa... na iya jefa kuri'ata," in ji Mohammad Asim Bhat, wani dan shekara 23 da ya jefa kuri'a a karon farko.
Hukumar Zabe ta ce kusan mutum miliyan tara aka yi wa rajistar zabe don zabar mambobin majalisar dokokin Jammu-Kashmir su 90.
An raba kujerun zuwa gida biyu da suka hadu suka yi yankin - 47 ga Kashmir da 43 ga Jammu.
'Yan takara 219 ne ke neman lashe kujerun mazabu 24 a zagayen farko na zaben, ciki har da 16 a kudancin Kashmir wanda sai a baya-bayan nan aka raba shi da 'yan bincigar da ke adawa da India.
Iyakokin da aka yi takara
Jammu da Kashmir yankin India ne mafi yawan Musulmai kuma tun 1947 yake fama da rikici da makociyarsu Pakistan.
India da Pakistan na ikirarin yankin nasu ne, bayan sun gwabza yaki na shekaru uku saboda yankin.
Har zuwa 2019, yankin Kashmir da ke karkashin ikon India na da 'yancin cin gashin kai, wanda Firaminista Narendra Modi ya ƙwace.
A shekarar da ta gabata Kotun Koli ta tabbatar da matakin da gwamnatin ta Modi ta dauka inda ta saka watan Satumban bana a matsayin lokacin gudanar da zabe.
Dawo da matsayi na musamman
Jam'iyyar BJP ta Modi ta ce kwace matsayin cin gashin kai na yankin ya dawo da zaman lafiya a yankin kuma na taimaka wa wajen cigaban sa.
A ranar Litinin din nan Modi ta shafin X ya bayyana cewa "A yayin da aka fara zagaye na farko na zaben Jammu da Kashmir, ina kira ga kowa da ya fita ya jefa kuri'a sannan ya goyi bayan karfafa dimokuradiyya."
A shekarun baya, kungiyoyin da ke fafutukar neman 'yanci na kai hare-hare kan zabuka a Kashmir, inda ake samun kin fitar masu jefa kuri'a.
Amma a zabukan watan Afrilu da Mayu yankin ya shaida fita jefa kuri'a mafi yawa a shekaru 35 inda kashi 58.46 na jama'a suka fita rumfunan zabe.
Ana yin fafatawar ta wannan karo tsakanin jam'iyyun yankin da suke alkawarin dawo da 'yancin kan yankin, da kuma jam'iyyar adawa da ke da kawance da kungiyoyin yankin, da kuma BJP, wadda ke son kawo cigaba da kawo karshen yaki da adawa.
Majalisar dokokin za ta samu ikon yin muhawara game da yankunan da suka shafi yankin, za su yi dokoki da amincewa da zartar da matakan gudanar da yankin, amma ba za ta iya dawo da matsayin musamman na cin gashin kai ba.