Ƴan sanda sun kama masu zanga-zanga a daidai lokacin da sauran jami'an ƴan sandan suka cikin jami'ar Columbia. / Hoto: Reuters

Guguwar zanga-zangar ɗalibai ta taso a Amurka inda ake yinta a jami’o’i da dama na Amurka inda ɗaliban ke kira ga jami’o’insu su yanke hulɗa da kamfanonin da ke da alaƙa da Isra’ila, inda a wasu jami’o’in ma, ana kira kan jami’o’in su yanke hulɗa da Isra’ilar baki ɗaya.

Zanga-zangar ɗaliban wadda rabon da a ga irin ta tun wadda aka yi a ƙasar a jami’o’i a lokacin yaƙin Vietnam tsakanin shekarun 1960 zuwa 1970 – wadda ta jawo aka kama ɗaruruwan ɗalibai.

Jami’ai na ƙoƙarin daƙile wannan zanga-zanga a daidai lokacin da ake shirin kawo ƙarshen zangon karatu na ƙarshe a jami’o’i.

Ga bayanai na baya-bayan nan dangane da zanga-zangar da ake yi a jami’o’in Amurka

Jami’ar Columbia

Jami'an 'yan sandan birnin New York da dama sun shiga Jami'ar Columbia tare da kame masu zanga-zangar, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito, yayin da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da ke wajen harabar jami'ar suka yi wa 'yan sanda masu dauke da makamai ba'a.

‘Yan sandan sun saka kimanin mutum 50 waɗanda suka kama cikin wata motar bas, kowannen su an daure hannuwansu a bayansu da igiya, duk wurin ya haskaka da fitulun motocin ‘yan sanda masu haske da ja da shudi.

Motocin daukar marasa lafiya da sauran motocin agajin gaggawa sun tsaya wurin.

Jim kadan kafin jami’an su shiga harabar jami’ar, ‘yan sandan New York sun samu sanarwa daga Columbia da ke ba jami’an izinin daukar mataki, kamar yadda wani jami’in tsaro ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Shugaban jami’ar, Minouche Shafik, ya bukaci ‘yan sanda da su ci gaba da zama a harabar har zuwa ranar 17 ga watan Mayu. Rundunar ‘yan sandan ta zo ne bayan jami’ar ta yi barazanar korar masu zanga-zangar.

Jami'an NYPD sun yi jigilar daliban da aka kama a cikin wata motar safa yayin da suke kokarin fitar da mutane daga wani gini da masu zanga-zangar neman goyon bayan Falasdinu suka yi a jami'ar Columbia.

Jami'ar Brown

Jami'ar Brown ta cimma yarjejeniya da daliban da ke zanga-zangar adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza domin kawo karshen zaman dirshen ɗin da suke ci gaba da yi a harabar makaranta tun ranar 24 ga watan Afrilu domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.

"Dalibai sun amince da kawo karshen zaman dirshen tare da guje wa wasu ayyuka da za su keta ka'idojin ɗa'ar Jami'ar Brown a karshen shekarar karatu," in ji Jami'ar Brown a cikin wata sanarwa.

Jami'ar ta amince da cewa za a gayyaci dalibai biyar don ganawa da mambobi biyar na Jami'ar Brown a watan Mayu don sauraron hujjojinsu kan dalilin da zai sa jami'ar ta janye daga Isra'ila.

"Bugu da ƙari, [Shugabar Jami'ar Brown Christina] Paxson za ta nemi Kwamitin Ba da Shawarwari kan Gudanawa na Jami'ar da ya ba da shawara game da batun yanke alaƙa zuwa ranar 30 ga Satumba,inda ake sa ran jami'ar za ta kaɗa kuri'a a taronta na Oktobar 2024. " a cewar jami'ar.

Jami'ar Havard

A cikin wata sanarwa, masu zanga-zangar sun ce jami'ar da ke Cambridge da Massachusetts "ta yi ƙoƙarin rufe duk wata hanya ta waje da kuma wata hanya zuwa wurin masu zaman na dirshen," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce "Sahen Gudanarwa na Harvard ya fara daukar matakin ladabtarwa kan dalibai da ma'aikatan dalibai kusan arba'in."

A makon da ya gabata, Harvard ta iyakance damar shiga sanannen wurin shaƙatawar nan nata ga waɗanda ke da shaidar makaranta bayan an kafa wani sansani na masu zanga-zanga.

Jami'ar Mexico

A Albuquerque, 'yan sanda cikin dabara sun tarwatsa tantuna tare da yin arangama na ɗan lokaci da masu zanga-zangar da suka mamaye ginin ƙungiyar ɗaliban Jami'ar New Mexico na kusan sa'o'i bakwai a daren Litinin zuwa safiyar Talata.

Jami’an jami’ar sun ce an kama mutum 16 da suka haɗa da ɗalibai biyar da kuma mutum11 da ba su da alaƙa da makarantar. Sun yi zargin cewa masu zanga-zangar sun lalata ginin kungiyar ɗalibai tare da fesa rubutun fentin a cikin harabar jami’ar. Sai dai ba su yi ƙiyasin adadin ɓarnar da aka yi ba nan take.

Jami'ar Jihar California, Humboldt

Masu zanga-zangar sun mamaye gine-gine biyu a makarantar Arewacin California. Gomman ƴan sanda masu sanye da hular kwano dauke da sanduna ne suka yi tattaki zuwa cikin harabar jami'ar tare da share duka zaurukan biyu. Jami'ar ta ce an kama mutum 25, kuma ba a samu raunuka ba.

Tun da farko jami'ar ta ba da sanarwar "rufewa," ma'ana ba a ba wa mutane izinin shiga ko zama a harabar ba tare da izini ba. Da karfe 3:24 na safe, shafin intanet na jami'ar ya bayar da umarnin neman mafaka ga mazauna jami'ar "saboda ci gaba da aikata laifuka a harabar."

An dage wannan odar bayan sa'o'i da yawa amma an gaya wa mazauna jami'ar su zauna a wuraren zama, cin abinci da kasuwanni.

Jami'ar Yale

Hukumomin Yale sun share matsugunin masu zanga-zangar bayan daliban sun yi biyayya ga gargaɗin karshe na su fice, in ji jami'an jami'ar.

Ba a bayar da rahoton kama mutane ba. Sai dai masu zanga-zangar sun bayyana a shafukan sada zumunta cewa za su mayar da zanga-znagar ta su zuwa wani yanki na gefen titi.

Jami'ar Connecticut

'Yan sanda sun shiga sansanin harabar makarantar a Storrs, Connecticut, kuma sun kama masu zanga-zangar bayan sun yi musu gargadi da yawa na su fice, in ji kakakin UConn Stephanie Reitz.

Kawo yanzu dai ba a samu adadin mutanen da aka kama ba, kuma jami’ai na ci gaba da aikin share fagen. Kamen dai ya zo ne kwana guda bayan shugabannin zanga-zangar sun gana da jami'an jami'ar.

Jami'ar Princeton

Shugaban jami'ar, Chris Eisgruber, ya wallafa wata sanarwa a shafin Instagram yana mai cewa an kama masu zanga-zangar 13 - 12 masu alaka da jami'ar - bayan da suka mamaye ɗakin taro na Clio na wani ɗan lokaci, wanda shi ne ɗakin taron da ake yaye ɗalibai.

Eisgruber a cikin sanarwar ya ce "Dukkan wadanda aka kama sun karbi sammaci saboda yin kutse kuma an hana su shiga harabar jami'ar."

"Daliban kuma za su fuskanci hukunci daga jami'ar, wanda zai iya kaiwa ga dakatarwa ko kora."

Northwestern University

Makarantar da ke Evanston, Illinois, ta ce ta cimma yarjejeniya da dalibai da malaman da ke wakiltar mafi yawan masu zanga-zangar a harabar ta tun ranar Alhamis.

Jami'ar a cikin wata sanarwa ta ce ta amince da amsa tambayoyi cikin kwanaki 30 game da "masu hannun jari da zuba jari a wasu kamfanoni, ciki har da wadanda jarin su ke goyon bayan wariyar launin fata na Isra'ila."

Har ila yau, ta ce za ta sake kiran wani kwamitin ba da shawara a wannan kaka "tare da babban burin tabbatar da cewa duk wani ɗan kasuwa da ya ci riba daga mamayar Isra'ila ba za a ba shi damar samar da ayyuka a harabar mu ba."

Sanarwar ta ce jami'ar na shirin tallafa wa malamai da daliban Falasdinawa da suke ziyara da kuma kara saka hannun jari wajen tallafawa rayuwar Musulmi da Yahudawa a harabar jami'ar.

Jami'ar ta Northwestern ta ce za ta ba da damar gudanar da zanga-zangar lumana da ta dace da manufofin jami'ar har zuwa ranar 1 ga watan Yuni, wanda shi ne karshen lokacin koyarwa a bazara. Jami'ar ta ce za ta bar tantunan agaji guda daya ne kawai, inda ta ce dole ne a cire duk wasu tantunan.

Jami'ar Texas

A wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a makarantar Austin da yammacin ranar Litinin, an daure mutane 79 da abin ya shafa a gidan yari, a cewar sashen shari’ar Travis County. An tuhumi akasarin su da laifin aikata laifuka.

Kimanin masu zanga-zangar 150 ne suka zauna a kasa yayin da jami’an jihar da ‘yan sanda suka kewaye su, inda daruruwan dalibai da masu zanga-zangar suka rika ihu lokacin da jami’ansu suka ja wani.

Bayan da ‘yan sanda suka tartwatsa asalin gungun masu zanga-zangar, daruruwan dalibai da masu zanga-zangar sun yi gudu don hana jami’an fita daga harabar jami’ar.

Masu zanga-zangar sun kai farmaki kan jami’an, inda suka haifar da dimbin gawarwakin mutane kafin ‘yan sanda su yi amfani da barkonon tsohuwa a kan jama’a tare da sanya na’urorin da za su bazu don share hanyar da wata motar daukar kaya ta dauke wadanda aka kama daga harabar jami’ar.

Jami'ar South California

Masu shirya sansanin sun gana da shugabar jami'ar Carol Folt na kusan mintuna 90 a ranar Litinin. Folt ta bayani dangane da abin da aka tattauna amma ta ce makasudin taron shi ne a ba ta damar jin damuwar masu zanga-zangar.

An shirya wani taro a ranar Talata. Jami'ar ta soke babban bikin yaye daliban da ta shirya yi a ranar 10 ga watan Mayu.

Tuni dai ta soke jawabin jami'in kula da masu goyon bayan Falasdinu na makarantar ya yi, saboda damuwa kan tsaro.

TRT World