Seakoo Wu na kallon bidiyon d aaka kirkira da kirkirarriyar basira da ke nuna fuskarsa dansa na magana, dan nasa ya rasu a shekarar da ta wuce yana da shekara 22 yayin da yake karatu a jami'ar Exeter da ke ingila. Hoto: AFP

A wata maƙabarta da ke gabashin China, wani mutum Seakoo Wu da ke cikin jimamin mutuwar ɗansa, ya ciro wayarsa, ya ajiye ta a kan dutsen kan kabari tare da kunna muryar ɗansa da aka taɓa naɗa.

Kalmomi ne da marigayin ɗansa nasa bai taba ambatar su ba, amma an samar da su ta hanyar ƙirƙirarriyar basira.

"Na san kana cikin tsananin takaici sosai a kowacce rana saboda ni, kuma ka rasa yaya za ka yi," in ji muryar mutum-mutumi da aka kwaikwayi ɗansa Xuanmo.

"Duk da cewa ba zan iya sake kasancewa a gefenka ba har abada a wannan duniyar, da kuma ci gaba da yi maka rakiya a rayuwa ba."

Wu da matarsa da baƙin ciki ya dame su, sun bi sahun 'yan kasar China da suka rungumi ƙirƙirarriyar basira wajen samar da surorin mamatansu, wadanda kamar a raye suke.

Wu na son ganin wani abu da zai maye gurbin ɗansa da ya riga ya mutu.

Wu ya ce "Da zarar mun haɗe duniyar nan da ta tsinkaye (meterverse), lallai yarona zai kasnace tare da ni a karo na biyu."

"Zan iya ba shi horo... ta yadda idan ya gan ni, zai san ni mahaifinsa ne."

Wasu kamfanonin China na ikirarin sun ƙirƙiri dubban matattun mutane a duniyar intanet da suke magana da motsi daga sakwan 30 zuwa sama.

Kwararru sun bayyana cewa za su iya kwantar da hankulan mutanen da suke cikin baƙin cikin rasa makusantansu.

Amma kuma sun kuma bayyana wata manufa ta dogara kan na'ura da tsarin Burtaniya na "Black Mirror" wanda ƙirƙirarriyar basira ce da ke iya rarrashin wanda aka yi wa mutuwa.

'Buƙata na kara yawa'

Wu da matarsa sun ɗimauce a lokacin da ɗansu daya tilo Xuanmo ya mutu, bayan mutuwar rabin jiki da ta same shi farar daya a shekarar da ta gabata a lokacin yana da shekara 22 a Jami'ar Exeter da yake karatu.

Wu ya ce "Dalibin da ke karanta harkokin kudi, mai sha'awar wasanni, ya yi rayuwa mai ƙayatarwa."

Ya fada wa AFP cewa "A ko yaushe yana ƙudirce son ya taimaki wasu da kuma umarnin aikata mai kyau da barin mummuna."

Sakamakon habakar da aka samu a fannin fasahar ƙere-ƙere kamar ChatGPT a China, Wu ya fara binciken hanyoyin da zai so ya dawo da yaronsa da ya mutu zuwa duniya.

Ya tattara hotuna da bidiyo da sautin murya na yaronsa, inda ya kashe dubban daloli yana daukar hayar kamfanonin ƙirƙirarriyar basira da suka sake ƙirƙirar fuska da muryar Xuanmo.

Sakamakon ya nuna ya zuwa yanzu ba a gama koyon wannan abu ba, amma kuma ya dauki hayar wasu mutanen da za su samar da wata ma'ajiya da ke dauke da bayanan dansa.

Wu na fatan za a samar da wani mutum a intanet da zai iya yin tunani da salon maganar ɗansa.

A 'yan shekarun nan a Amurka akwai kamfanoni da dama suka ƙware wajen samar da "surorin fatalwa".

Amma kuma wannan kasuwa na haɓaka sosai a China, kamar yadda Zhang Zewei, wanda ya kafa kamfanin ƙirƙirarriyar basira na 'Super Brain' kuma tsohon abokin aikin Wu ya bayyana.

"Game da fasahar ƙirƙirarriyar basira, China na kan gaba a duniya baki ɗaya," in ji Zhang da ya fito daha garin Jingjiang na gabashin kasar.

"Kuma akwai mutane da yawa a China, da yawan su suna da bukatu a zuƙatansu, wanda ke ba mu dama idan ana batun sayar da kayanmu."

Kamfanin Super Brain na cajin tsakanin dala 1,400 da dala 2,800 don ƙirƙirar surar avatar a cikin kwanaki 20, in ji Zhang.

Wadannan avatar sun hada da na wadanda suka mutu suka bar iyayensu, kuma ba su rayu da su sosai ba, da ma na samarin da suka mutu suka bar 'yan matansu.

Kwastomomi na iya magana ko yin waya ta bidiyo da mutumin da ya hau kan muryar mamacinsu.

Zhang ya ce "Muhimmanci ne... duniyar na da girma."

"Nau'in mutum na intane zai iya zama har abada, har ma bayan an rasa gangar jikinsa."

'Sabuwar halitta'

Sima Huapeng, wanda ya kafa kamfanin 'Silicon Intelligence' da ke Nanjing ya ce fasahar za ta kawo wani nau'i na sabuwar halittar ɗan'adam.

Ya kwatanta hakan da kamar sura ce ta hoto da kamantawa, wadda ke taimakawa mutane wajen tunawa da mamata ta sabuwar hanya.

Tal Morse, wani mai bincike a Cibiyar Mutuwa da Zamantakewa da ke Jami'ar Bath ta Ingila ya ce wadannan fatalwoyi na iya sanyaya zukatan 'yan'uwan mamaci.

Amma ya yi gargadi da cewar ana bukatar gudanar da bincike don ganon tasirinsu ga ƙwaƙwalen ɗan'adam, da kuma ko sun dace da al'ada ko a'a.

Morse ya shaida wa AFP cewa "Babbar tambaya a nan ita ce... ta yaya wadannan surori ko fatalwoyi za su zama masu biyayya ga mutanen da aka samarwa da su."

"Me zai faru idan suka yi abubuwa da za su lalata yadda za a tuna mutumin da ake son su maye gurbi?"

Kwararru na cewa wata matsalar kuma ita ce yadda ba a samun yardar wadanda suka mutu din.

A yayin da ba lallai ne sai an samu izini kafin a kwaikwayi magana ko halayya ba, amma za a iya neman a yi wasu abubuwa na duniyar tunani," in ji Nate Sharadin, masanin falsafa a Jami'ar Hong Kong kuma ya kware kan ƙirƙirarriyar basira da tasirinta kan zamantakewa.

A wajen kamfanin Super Brain na Zhang, duk wata fasaha ta zamani "na da harshe biyu ne".

"Matukar muna taimaka wa masu bukata, to mu ba mu da matsala."

Ba ya aiki da wadanda suke ganin za su samu cutuwa ba, ya bayar da misalin wata mace da ta so kashe kanta bayan 'yarta ta rasu.

Wu da ke jimamin rasa dansa, ya ce watakila Xuanmo zai iya neman a dawo da shi rayuwa ta hanyar suranta shi a yanar gizo.

"Wata rana, yarona, za mu sake haduwa a duniyar metaverse," in ji shi a yayin da matarsa ke zubar da hawaye.

"Fasahar kera wadannan mutane na yanar gizo na kara habaa kowacce rana... Kawai magana ake ta lokaci."

TRT World