Aiki tare da manufar juyin juya hali a ayyukan sojin Iran sun zama abin lura sosai, inda a wasu lokutan suke jawo hankulan yankuna da kasashen duniya.
A tarihi, shirin makami mai linzami na Iran ya kasance wani babban tashin hankali ga jami'an diflomasiyyar Kasashen Yamma.
Ko da yake, a 'yan shekarun nan, saka hannayen jarin Tehran da kuma ci gabanta a na'urorin jirgaren sama mara matuka UAV ya taimaka wajen kara haskakata a idon duniya.
Kazalika karuwar sayen jirage marasa matuka UAV na Iran da wasu masu hannu da shuni ke yi ya taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa rikici a yankin.
Kasashe daban-daban, wadanda ke ƙera jirage marasa matuka da ke dauke da makamai sun yi musayar fasaha tare da sayar da kayayyakinsu, sai dai samar da jiragen ga wadanda ba na gwamnati ba ya ƙara haifar da wani sabon salo a arangamar soji.
Duk da rashin fasaha da kayan aiki na zamani, jiragen Iran UAV ba su kai na sauran kasashe da dama ba, ana kuma bayyana su a matsayin ayyukan da suka yi nasara ta fuskar farfaganda.
Sai dai, bincike sun yi nuni da cewa, a zahirie ba sa gudanar da ayyukan da ake sa ran za su yi, kamar yadda rahotanni daga sojojin Ukraine suka tabbatar da cewa za a iya saukar da jiragen na UAV cikin sauƙi ko da kuwa da ƙananan makamai daga nisan kilomita.
A hakikanin gasikya, a maimakon ayyukan UAV na Iran su kasance nasara a fannin fasahar zamani na soji, sai suka zama wani bangare da ya yi fice wajen zurfafa rikice-rikicen yankin, wadanda kungiyoyin da ba na gwamnati ba ke yawan amfani da su akai-akai a matsayin makami na yaɗa farfaganda na juyin juya hali da fadada batutuwan da suka shafi Iran.
Yawan gayya ya ta'allaka ga ƙarfin da za a samu
Wani muhimmin matakin tsaro da Iran ke amfani da shi a dabarun kariyarta na ''Swarming Tactic'' shi ne gayya wajen amfani da jirage marasa matuka UAV da kuma rokoki kai tsaye zuwa kan makiyanta.
Jami'an Iran suna sane da cewa sojojinsu ba za su iya karawa da sojojin Amurka da na Isra'ila ba yakin basasa.
Don haka, Iran ta ɗauki dabarun tsaro da aka fi sani da ''Swarming Tactic'' gayya, wanda ke da nasaba da tsaro da kai hare-haren gayya.
A bangaren Iran, hanya mafi dacewa wajen kai hari kan sansanonin Amurka da jiragen yakinta a yayin harin soji a kasar ita ce ta harba makamai masu linzami da jiragen yaki na UAV.
Wannan dabarar, wacce 'yan Houthi masu alaka da Iran suka yi nasarar kaddamarwa kan Saudiyya, makasudinsa shi ne ya haifar da rikici tare da shata layi a fadin yankunan kasar, musamman ta hanyar amfani da 'yan kungiyoyin Shi'a da aka fi sani da Resistance Axis.
Daya daga cikin kayan aikin da wadannan kungiyoyin Shi'an ke sa ran za su yi amfani da su a cikin tsarin dabarun gayyar shi ne jiragen yakin Iran na UAV, musamman jirage marasa matuka kirar Shahed.
Hare-haren jiragen yakin Iran na UAV
Daga cikin jiragen yaki marasa matuka UAVs da sojojin Iran suka kirkiro, wadanda suka fi aiki daga cikinsu sune kirar Ababil-3 da Mohajer-6 da Saegheh da Shahed, da H-110 Sarir, da Fotros da Karrar, da kuma Kaman-22 UAVs.
kirar Jiragen yaki na Shahed sun fi daukar hankalin kafafen yada labarai na duniya saboda amfani da su da sojojin Rasha suke yi a yakin Ukraine da ake ci gaba da yi.
Alal misali, wani rahoto da Rundunar Sojin Sama na Ukraine ta fitar a ranar 21 ga watan Disamba, 2023, ta yi ikirarin cewa Rasha ta kai wa Ukraine hari da jiragen Shaheed UAV guda 3,700 kirar Iran a yakin kusan shekaru biyu.
A wannan ranar ne cikin wani shirin talabijin da aka yi da shi, mai magana da yawun rundunar sojin saman Ukraine Yurii Ihnat ya bayyana cewa, "a kowane dare, yankuna 10 zuwa 15 suna fuskantar hare-hare daga jiragen yakin Shaheed na UAV", yana mai cewa, sojojin saman Ukraine sun yi nasarar kakkaɓo jiragen yaƙi 2,900 da Rasha ta harba.
A cewar bayanan da wata majiya mai tushe ta fitar, Moscow ta soma amfani da jiragen Shaheed UAV na Iran a yakin Rasha da Ukraine wanda aka fara tun a watan Satumban 2022.
Sai dai Iran ta yi fatali da wadannan ikirari ta hanyar tabbatar da cewa ta sayar da wadannan jiragen ne ga kasar Rasha kafin ɓarkewar yaƙin.
Siffofin jirgi kirar Shaheed UAV
Samfuran jiragen Shahed UAV, wanda masana'antun kera jiragen sama na Shahid Aviation suka kirkira, sun hada da sanannun samfura irin su Shahed 129 da Shahed 136 da Shahed 171 da Shahed 181da Shahed 191 da Shahed 149 da Shahed 147 da Shahed 238 wadanda suk sun taka muhimmiyar rawa a rikice-rikicen yankin.
Dangane da ƙayyadaddun fasahohi, kirar UAV Shahed 129 yana da tsayin da ya kai mita 8 da fikafikan da tsayinsu ya kai mita 16.
Yana aiki da injin din Rotax 914 kuma yana ɗaukar bama-bamai guda huɗu kirar Sadid-345 masu nauyin kilogiram 400.
A cewar Janar Amir Ali Hajizadeh, kwamandan dakarun kare juyin juya halin Iran, jirgin ruwa na Shaheed 129 UAV ya kai nauyin kilomita 1,700, sannan tsayinsa daga kasa ya kai ƙafa 25,000.
An yi amfani da wannan kirar jirgin na UAV sosai a Siriya.
Samfurin jirgin Shaheed 136 UAV da aka siffanta shi jirgin yaki mara matuki ''kamikaze UAV'', an yi zargin cewa an kirkiro shi ne bisa ga samfurin jirgin Isra'ila na Harpy UAV.
Yana da tsayin da ya kai mita 3.5 sannan nauyinsa ya kai kilogiram 200, yana gudun da ya kai kilomita 185 cikin sa'a daya da nisan kilomita 2,000. An yi amfani da shi sosai a yakin Rasha da Ukraine.
Afkuwar Bala'i
Ana sa ran amfanin jiragen Shaheed UAV waɗanda suka taka rawa sosai a rikice-rikicen yankuna a ƴan shekarun da suka gabata, za su ƙara yawa tare da daukar wasu samu sabbin salo.
Rikici tsakanin kungiyoyin 'yan Shi'a da ke samun goyon bayan Iran da sojojin Amurka ya karu a sakamakon yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.
A karon farko, cibiyoyin kungiyoyin 'yan Shi'a da ke samun goyon bayan Iran a Iraƙi da Siriya, da kuma Yemen sun fuskanci munanan hare-hare daga Amurka.
Wata tambaya mai mahimmanci a nan ita ce ko kungiyoyin 'yan Shi'a za su ɗaga wa Amurka kafa? Idan har waɗannan ƙungiyoyin ba su ɗaga wa Amurka kafa ba, akwai yiwuwar za a ci gaba da kai wa sansanoninta hare-hare da wadannan jiragen yaki na Shaheed UAV.
A irin wannan yanayin da ake ciki, idan har aka ci gaba da kai hare-hare kan sojojin Amurka a Iraƙi da Siriya, akwai yiwuwar a sanya masana'antun ƙera jiragen sama mara matuƙa na Shahed UAV da ke Iran cikin jerin abubuwan da za a tattauna a dakin taro na John F. Kennedy da ke Fadar White House.