Rikicin Isra’ila da Falasdinu da ke faruwa a halin yanzu zai yi matukar tasiri ta hanyoyi da dama musamman wajen tayar da zaune tsaye.
Babu wani manazarci mai hikima da zai iya hasashen yadda dangantaka tsakanin yankin Gabas ta Tsakiya da lamarin ya shafa da kuma sauran kasashen duniya za ta kasance bayan ura ta lafa, domin kuwa komai na iya faruwa a gaba.
Amma duk da haka, akwai yiwuwar Washington ta iya mai da hankalinta sosai ga yankin Gabas ta Tsakiya, yin hakan watakila zai iya kau da hankalin Amurka da sadaukar da kanta da kuma gwagwarmayarta ga Ukraine.
Tun bayan kaddamar da "Operation Al Aqsa" da Hamas ta yi a ranar 7 ga Oktoba, muhawara ta barke kan harin tsakanin 'yan majalisa a Washington inda wasu ke cewa "yakin addini" da kuma "tsantsar mugunta" ce daga Hamas, shigen irin kalaman da George W. Bush "Yaki da Ta'addanci" da yake yawan amfani su a zamaninsa.
Kamar sauran magabatansa, Shugaba Joe Biden da gwamnatinsa sun bi sahu ta fuskar tallafawa Isra'ila.
Biden da wadanda ke jikinsa sun bayyana wa duniya cewa babu wani labule da ke tsakanin Washington da Tel Aviv.
Amurka dai ta aika jirgin yakinta yankin Gabar Tekun Gaza da aka yi wa kawanya, sannan ta tura wani sako mai karfi game da kasancewar sojojin yaƙinta a yankin Gabas ta Tsakiya tare da nuna goyon bayanta ga Isra'ila, yayin da ake ci gaba da kashe rayuka da kuma jefa mutanen Gaza miliyan 2.3 (wadanda rabinsu yara ne) cikin uƙuba.
A ranar Laraba ne Biden ya kai ziyarar nuna goyon bayan kasarsa ga dadaddiyar abokiyarta Isra'ila.
Duk da haka, manufofin Amurka game da Isra'ila da Falasdinu ba za su zo daya da matsayar al'ummar Larabawa ba, irin labaran da manyan kafofin yada labarai na Washington da wadanda ke tsakanin al'ummomin Larabawa ke yadawa game da gwagwarmayar Falasdinawa sun bambanta da zahirin abun da ke faruwa.
Sakamakon wannan rikici da ya matukar daukar hankalin duniya, akwai yiwuwar Amurka ta fuskaci ƙarin adawa a yankin Larabawa da sauran kasashen Musulmai a lokuta masu zuwa.
"Kawo yanzu dai gwamnatin (Biden) ba ta fito ƙarara ta bayyana matsayar Amurka ta goyon bayan a kawo karshen rikicin ba, yin hakan kuwa zai bayyana siyasar da ke cikin rikicin,'' kamar yadda Ferial Saeed, wani tsohon babban jami'in diflomasiyyar Amurka ya bayyana wa TRT World.
“Ba tare da fitowa ta bayyana matsayarta ba, amfani da ƙarfin soji zai haifar da babban kalubale ga Washington domin al'amura za su kara tabarbarewa ga bangarorin biyu da kuma yankin, sakamakon haka kuma akwai yiwuwa a zargi Amurka da rawar da ta taka wajen jagorantar martanin kasashen duniya.”
Akwai dalilai da dama da ke nuna cewa China da Rasha za su yi amfani da damar adawa da Amurkawa da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan tashin hankalin da Isra'ila da ta samu goyon bayan Amurka ta jefa yankin.
Duk da cewa Beijing da Moscow sun ƙulla kyakkyawar alaka da Tel Aviv, amma China da Rasha sun dage wajen nuna goyon bayan warware batun Falasdinawa bisa tsarin dokokin kasa da kasa, yayin da suke adawa da mamayar Isra'ila.
Kazalika, duka kasashen ba su fito fili sun ayyana Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci ba, a maimakon haka suna kallonta a matsayin halastacciyar kungiyar gwagwarmaya.
A bangare guda, Beijing da Moscow sun yi nasara wajen inganta kyakkyawar danganta da Isra'ila a tsawon shekaru, sannan ba su ɓata hanyar da za ta cutar da alakarsu da kasashen ''Larabawa ba".
A daidai lokacin da ake cigaba da yakin nan, hukomomi a birnin Beijing da Moscow sun samu damar kushe yadda Amurka ta yi wa rikicin sakainar kashi tare da bayyana yadda Amurkar ke daukar bangare a yakin Falasdinawa da Isra’ila. Akwai darussa masu yawa a wannan lamarin.
A lokacin da ake tsaka da yaki tsakanin Hamas da Isra’ila a shekarar 2021, Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi ya soki Amurka da dakatar da wata sanarwa ta Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wadda da Amurkar ta bari, da an saukin rikicin.
Lallai, a jiya matsayar da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar tare da kasar Rasha, wadda ta samu goyon bayan China ta kira da a tsagaita wuta saboda ayyukan jin kai, ta samu cikas ne saboda Amurka da Faransa da Japan da Birtaniya sun ki amincewa, sannan kasashe shida; (Albaniya, Brazil, Ecuador, Ghana, Malta da Switzerland) sun kaurace wa taron.
Dama can Amurka ta dade tana nuna rashin jin dadinta a kan yadda kasar China ta yi amfani da karfin ikon da take da shi na kujerar naki a wurare irin Syria da Sudan da Myanmar.
Watsi da matsayar da Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar inda ta yi Allah wadai da Isra’ila da Amurka ta yi, dama ce ga China domin nuna wa duniya cewa ta fi Amurka tausayi da hankali da saukin mu’amala.
Kwana uku bayan Hamas ta kaddamar da hare-haren da ta sanya wa suna Ambalisar Kudus wato “Operation Al Aqsa Flood”, Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana damuwarsa a kan yawaitar kashe-kashen da ke wakana a Isra’ila da Falasdin a wata ganawa da ya yi da Firaiministan Iraqi Mohammed Shia al Sudani lokacin da ya ziyarci birnin Moscow.
Putin ya nanata cewa tabbatar da ‘yantacciyar kasar Falasdin yana da matukar muhimmanci, sannan ya zargi Amurka da hannu a zubar da jinin da ke wakana. “Ina tunanin mutane da dama za su amince da ni cewa akwai sakacin Amurka a rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya,” inji shi.
Haka kuma kasancewar Rasha na cigaba da gwabza yaki da kasar Ukraine, hukomomin kasar za su yi farin cikin samun damar kawar da idon duniya daga gare ta, domin a mayar da hankali zuwa yakin na Isra’ila da Falasdin, wanda hakan zai sa ta samu ragowar sukar da take sha a game da afkawa makwabciyarta Ukraine da yaki da ta yi kusan wata 20 da suka gabata.
Babu makawa masu ruwa da tsaki a Rasha za su cigaba da bibiyar abin da Amurka za ta yi a game da yakin na Isra’ila da Falasdin, tare da tsammanin yakin zai amfane ta a nata yakin da Ukraine.
“Russia hopes that the crisis will diminish US support for Ukraine,” said Gordon Gray, a former US ambassador to Tunisia, in an interview with TRT World.
“Rasha na da burin ganin yakin ya sa Amurka ta daina taimakon Ukraine, inji tsohon Ambasadan Amurka a Tunisaia Gordon Gray, a zantawarsa da TRT.
“Amma Rasha za ta bi a hankali ne saboda ba za ta so mu’amalarta da Isra’aila ta lalace ba, wadda har yanzu ba ta fito fili ta goyi bayan Ukraine ba.”
A karshe,yadda duniyar take kara rarrabuwa, China da Rasha suna ta kokarin ganin suna bin hanyoyin samar da maslaha a rikice-rikicen da suke faruwa a duniya da nufin samun karin magoya baya a yankin Asia da Gabas ta Tsakiya da kasashen Kudancin Amurka da bayyana yadda jijji da kan Amurka da rashin tsarin diflomasiyya mai kyau ke jawo matsaloli a yankuna da dama.
A yanzu da kasashen BRICS, wato Brazil da Rasha da Indiya da China da Afirka ta Kudu suke kara samun magoya baya da kuma yadda Beijing da Moscow ke kara nuna kansu a matsayin masu kare Falasdin, hakan zai sa su samu karbuwa sosai a kasashen masu raunin tattali arziki da ake kira kasashen Global South.
A yanzu da kasashen China da Rasha suka bayyana ra’ayi daban da kasar Amurka a game da yakin Isra’ila da Falasdin, kasashen Labarawa za su kara amincewa da kasashen biyu sama da Amurka.