UNIFIL ta yi Allah wadai da sojin Isra’ila kan rushe layin da ya shata wajen janyewa tsakaninta da Lebanon

UNIFIL ta yi Allah wadai da sojin Isra’ila kan rushe layin da ya shata wajen janyewa tsakaninta da Lebanon

UNIFIL ta yi tir da matakin a matsayin “tsantsar saɓa ƙuduri na 1701 da dokokin duniya.”
“Muna kira ga duka ɓangarorin su kauce wa ɗaukan duk wani mataki, ciki har da rusa kayayyakin fararen hula da gine-gine, wanda zai kawo matsala ga tsagaita wuta,” a cewar dakarun na Majalisar Ɗinkin Duniya. / Hoto: AA Archive

Rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya ta wucin-gadi a Lebanon (UNIFIl) ta yi Allah wadai da rushe hasumiyar tsaro ta sojojin Lebanon da sojojin Isra'ila suka yi da kuma janye shuɗin shinge, wanda ya shata layin janyewa tsakanin Lebanon da Isra’ila.

A cewar wata sanarwa da UNIFIL ta fitar ranar Asabar, dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun lura da wata motar rushe gine-gine ta Isra'ila tana rushe wani shuɗin shinge da ke nuna layin janyewa tsakanin Lebanon da Isra'ila a Labbouneh.

Ta ƙara da cewa motar ta kuma lalata "hasumiya da sojojin Lebanon ke amfani da ita wajen sanya ido, wacce take dab da wajen da UNIFIL take."

UNIFIL ta yi Allah wadai da lamarin da kakkausar murya, inda ta bayyana cewa "lalata kadarorin UNIFIL da aka yi musu alama a bayyane da ginin na rundunar sojojin Lebanon da Isra’ila ta yi da gangan kuma kai tsaye, wani babban cin zarafi ne ga ƙudiri mai lamba 1701 da dokokin ƙasa da ƙasa."

"Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su guji duk wani mataki da suka haɗa da lalata dukiyoyin fararen hula da ababen more rayuwa da ka iya kawo cikas ga tsagaita buɗe wuta," in ji rundunar ta MDD.

Saɓa yarjejeniyar da Isra’ila ta yi

Ƙudirin Kwamitin Tsaro na MDD mai lamba 1701 da aka amince da shi a ranar 11 ga watan Agustan shekara ta 2006 ya yi kira da a dakatar da yaƙin da ake yi tsakanin ƙungiyar Hezbollah da Isra'ila da kuma samar da yankin da ba shi da makamai a tsakanin Shuɗin Layi da kogin Litani da ke kudancin Labanon, in da sojojin Lebanon da UNIFIL za su kasance a wajen.

Ya zuwa yammacin Asabar, Isra'ila ta aikata laifuka 383 na saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane 32 tare da jikkata 39, a cewar wasu alƙaluma da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya fitar bisa aiki da bayanan da hukumomin Lebanon suka bayar.

A ƙarƙashin yarjejeniyar ta tsagaita bude wuta, Isra'ila za ta janye sojojinta zuwa kudancin Shuɗin Layin - kan iyaka - a matakai, yayin da rundunar sojan Lebanon za za ta tura dakaru kudancin Lebanon cikin kwanaki 60.

Bayanai daga ma'aikatar lafiya ta Lebanon na nuni da cewa tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare Lebanon a ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2023, an kashe aƙalla mutane 4,063 da suka haɗa da mata da ƙananan yara da ma'aikatan lafiya, yayin da wasu 16,664 suka samu raunuka.

TRT World