Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters

1221 Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta kai hari sansanonin soji da dama a arewacin Isra’ila a ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar fargaba tsakanin ɓangarorin biyu.

Hezbollah ta bayyana cewa mayaƙanta sun kai hari Marj “da makaman da suka dace,” wanda hakan ya yi sanadin hari ya faɗa kai tsaye.

Haka kuma ƙungiyar ta kai hari kai tsaye da makamai masu linzami kan sansanonin Barakat Risha da al-Raheb, inda ta ce ta kai harin ne domin nuna goyon baya ga jama’ar Falasɗinawa.

Babu martani kai tsaye daga rundunar sojin ta Isra’ila dangane da wannan harin.

0610 GMT — Sojojin Isra'ila sun umarci mazauna Khan Younis su yi hijira daga unguwar Al Jalaa wanda a baya wuri ne da sojojin suka ayyana a matsayin "yanki mai aminci".

Unguwar Al-Jalaa ba za ta ci gaba da kasancewa a matsayin “wuri mai aminci ba,” in ji sanarwar sojojin.

Ta yi iƙirarin cewa mayaƙan Hamas na “aiki” daga unguwar tare da cewa wurin zai kasance “wuri mai hatsari na yaƙi.”

Duk da cewa a baya sojojin Isra’ila sun rinƙa ayyana wasu wuraren a matsayin “masu aminci,” amma suna ci gaba da kai munanan hare-hare a wuraren tare da jawo mutuwar Falasɗinawa da dama.

TRT Afrika da abokan hulda