Ministan Harkokin Wajen Brazil Mauro Vieira yayin da yake ganawa da manema labarai a karshen taron Ministocin Kungiyar Kasashe Masu Karfin Tattalin Arziki ta G20 a birnin Rio de Janeiro. Hoto: AFP

Bakin Ƙasashe Masu Ƙarfin Tattalin Arziki na G20 kan goyon bayan samar da mafita ta ƙasashe biyu masu cin gashin kansu ya zo ɗaya, a matsayin hanyar kawo ƙarshen yaƙin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, in ji Brazil wadda take karɓar baƙuncin wani taro da manyan jami’an diflomasiyya.

Abin da ya kara matsin lamba kan Isra’ila kan ta amince da ’yancin kasar Falasdinawa. Goyon bayan samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu da Kungiyar G20 ta yi a ranar Alhamis ya zo ne kwana daya bayan da Majalisar Dokokin Isra’ila ta kada kuri’ar adawa da amincewa da kasancewa kasar Falasdinawa a matsayin kasa mai ’yanci, abin da ya sa Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce “ya aika da babban sako ga kasashe duniya.”

Batun yakin da Isra’ila take yi a Gaza da ta mamaye shi ne babban abin da ya mamaye taron Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar G20 a birnin Rio de Janeiro, da kuma batun yakin Rasha da Ukraine da kuma rashin tasirin Majalisar Dinkin Duniya da sauran manyan cibiyoyin duniya da rarrabuwar kawunan da ake fuskanta.

“Baki ya zo daya” dangane da batun samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu “a matsayin ita ce mafita daya tilo a yankin Gabas ta Tsakiya,” kamar yadda Firaiministan Harkokin Wajen Brazil Mauro Vieira ya shaida wa manema labarai.

“Dalili daya da ya sa [Vieira] bai ce gaba daya baki ya zo daya shi ne ba kowane mai jawabi ne ya yi magana kan batun,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito Ma’aikatar Harkokin Wajen Brazil na cewa.

“Kowane [minista] da ya yi jawabi ya nuna goyon baya” kan batun samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, kuma “galibi ministocin ne,” in ji shi.

‘Kowa na goyon bayan samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu’

Taron ya samu halartar manyan jami’an diflomasiyya ciki har da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov da Babban Jami’in Diflomasiyyar kasar Turkiyya Hakan Fidan da Babban Jami’in Tsare-tsare na Tarayyar Turai (EU) Josep Borrell.

Borrell ya bukaci Viera ya yi amfani da sanarwar rufe taron kan “yi wa duniya bayani kan cewa yayin taron Kungiyar G20, kowa yana goyon bayan” kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu da kasancewar kasar Falasdinawa a kusa da Isra’ila.

“Kowa da kowa a nan, ban ji wani ya ce bai amince ba. Wannan babbar bukata ce ta samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu,” kamar yadda Borrell ya shaida wa manema labara.

“Babban abin lura shi ne Isra’ila ba za a taba samun zaman lafiya ba, har sai an ba Falasdinawa ’yanci kuma sun samu ’yancin gina kasarsu ta kansu.”

Yakin Isra’ila a Gaza

Fiye da wata hudu bayan fara yaki a Gaza da aka mamaye, wanda a kullum ake fargabar shiga mummunan halin jin-kai, Isra’ila tana ci gaba da fuskantar karin matsin lamba kan dacewar amincewa da kasancewar kasar Falasdinawa – har daga manyan kawayenta kamar kasar Amurka.

Kimanin kaso 72 cikin 100 na kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya sun amince da kasar Falasdinu.

Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 29,410 galibi mata da kananan yara kuma akalla mutum 69,465 ne suka jikkata a yakin da ake ci gaba da yi a Gaza.

Kaso 85 cikin 100 na mutanen da ke yankin Gaza da aka mamaye sun kaurace wa gidajensu saboda hare-haren da Isra’ila take kai wa kan mai uwa da wabi kuma duka al’ummar Gaza tana fuskantar matsalar karancin abinci.

13 cikin 34 na asibitocin yankin suna aiki ne rabi da rabi saboda yakin.

TRT World