Jami’an tsaron Turkiyya sun “kawar da” ‘yan ta’adda sama da 2,000 tun daga farkon shekarar 2023, kamar yadda ministan tsaron kasar Yasar Guler ya fada.
A bayanin da ya yi wa Majalisar Dokokin Turkiyya ranar Laraba, Guler ya bayyana nasarorin da Ankara ta samu a yaki da ta’addanci ciki har da yaki da 'yan ta’adda a kasashe makwabta irin su Arewacin Syria da Iraki.
Guler ya bayyana cewa Turkiyya ta fi samun nasara a yaki da ta’addanci cikin wannan shekarar. Akalla ‘yan ta’adda 2,067 aka kawar kawo yanzu cikin wannan shekarar, in ji shi.
“Mun kaddamar da dukkan ayyukanmu a Syria da Iraki ne bisa ‘yancin kare kai na sashe na 51 na dokar Majalisar Dinkin Duniya, tare da mutunta ‘yancin kan makwabtanmu,” kamar yadda Yasar ya bayyana.
“A lokacin shirya ayyukan, an dauki dukkan matakai na kauce wa taba fararen-hula da ba su ji ba ba su gani ba da kawayenmu da kuma ababen tarihi da al’adu tare da muhalli,” in ji shi.
Nasarar yakar ‘yan ta’adda
Jami’an Turkiyya suna amfani da kalmar "kawarwa" don nuna cewa dan ta’addan ya mika wuya ko an kashe shi ko kuma an kama shi.
‘Yan ta’addan YPG/PKK sukan buya a arewacin Syria da kuma Iraki inda suke shirya hare-hare kan dakarun Turkiyya ko kuma kan jama’a.
Tun shekarar 2016, Ankara ta kaddamar da shirye-shirye uku kan ta’addanci a Arewacin Syria domin hana wanzuwar ta’addanci don mutane su zauna lafiya. Wadannan hare-haren sun hada da: Euphrates Shield (a shekarar 2016) da Olive Branch (a shekarar 2018) da kuma Peace Spring (a shekarar 2019).
Turkiyya ta kaddamar da atisayen Operation Claw-Lock a watan Afrilun 2022 a maboyar kungiyar ‘yan ta’adda ta PKK da ke Iraki a lardunan Arewacin Metina da Zap da kuma Avasin-Basyan kusa da bakin iyakan Turkiyya.
Kafin wannan an yi atisayen Operations Claw-Tiger da Claw-Eagle, da aka kaddamar a shekarar 2020 domin kawar da ‘yan ta’adda da ke buya a arewacin Iraki inda suke kitsa hare-haren ketare a Turkiyya.
A shekaru 35 da ta yi tana kaddamar da hare-haren ta’addanci a Turkiyya, kungiyar PKK – wadda Turkiyya da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci – ta janyo mutuwar sama da mutum 40,000, ciki har da mata da yara da jarirai. Kungiyar YPG ce reshenta ta Syria.