1547 GMT — Turkiyya na aiki don kwashe karin marasa lafiya 50 daga Gaza, in ji ministan lafiya
Turkiyya ta ce ta shirya jerin sunayen majinyata 50 galibi yara kanana da za ta kwashe daga Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda aka shafe kwanaki 46 ana kai hare-hare ba kakkautawa.
Bayan da Turkiyya ta karbi rukuni biyu na jimlar marasa lafiya 88 daga yankin Falasdinawa da aka mamaye a cikin makonnin da suka gabata, Ministan Lafiya Fahrettin Koca ya ce za a iya kwashe na uku a cikin kwanaki masu zuwa.
Koca ya shaida wa 'yan majalisar dokokin Turkiyya a majalisar dokokin kasar a Ankara babban birnin kasar cewa, "Za a iya kai dauki na uku a cikin kwanaki masu zuwa," yana mai cewa kasra za ta fi ba da muhimmanci wajen kwashe jarirai da yara da marasa lafiya.
Ya ce tare da majinyatan 88, Turkiyya ta karbi jimillar mutane 150 daga Gaza da suka hada da abokai 62, ya ce majinyata shida na samun kulawa a sashen kula na musamman.
Da aka tambaye shi game da kwashe jarirai bakwaini a Gaza, sai ya ce suna shirin fara kwashe jarirai ‘yan kasa da watanni 12 da yara ‘yan kasa da shekaru hudu.
1432 GMT — Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki da 'kisan kare dangi'
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki da "kisan kare dangi" a Gaza, yayin da ya jagoranci wani babban taron kungiyar kasashen BRICS.
Pretoria tana karbar bakuncin taron BRICS - kungiyar manyan kasashe masu tasowa wadanda suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da China, da Afirka ta Kudu - da nufin samar da martani daya ga rikicin Isra'ila da Falasdinu.
"Hukuncin gama-gari da ake yi wa Falasdinawa fararen hula ta hanyar amfani da karfi da Isra'ila ke yi ba bisa ka'ida ba laifi ne na yaki. Hana magunguna da man fetur da abinci da ruwa ga mazauna Gaza da gangan, tamkar kisan kiyashi ne," in ji Ramaphosa.
1353 GMT — Ana samun ci gaba a 'yantar da mutanen da ake garkuwa da su a Gaza — Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "muna samun ci gaba" kan dawo da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba, bayan masu shiga tsakani sun ce ana shirin sasantawa.
"Ina fatan za a samu labari mai dadi nan ba da jimawa ba," Netanyahu ya fadawa sojojin Isra'ila a wani sansanin soji da ke arewacin kasar
Jim kadan bayan haka, ofishinsa ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa, "bisa la'akari da ci gaban da aka samu dangane da sako mutanenmu da aka yi garkuwa da su", majalisar ministocin yaƙi da na tsaro da kuma gwamnati za su yi taro a jere a yammacin ranar Talata.
Kalaman na zuwa ne bayan da shugaban Hamas da kuma babbar mai shiga tsakani Qatar duk suka ce akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu da Isra'ila.
1350 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan jarida biyu a kudancin Lebanon
Isra’ila ta kashe ‘yan jarida biyu wadanda suke aiki da gidan talabijin na Al-Mayadeen a yankin Tayr Harfa da ke kudancin Lebanon.
Gidan talabijin din ya fitar da sanarwa inda ya yi ta’aziyyar rasuwar wakiliyarsa Farah Omar da kuma mai daukar hotonta Rabie Al-Maamari.
Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ruwaito firaiministan kasar Najib Mikati yana Allah wadai da kisan ‘yan jaridar.
Kamfanin dillancin labarai na Al-Quds da ke da alaka da Hamas ya wallafa hotunan 'yan jaridar biyu a shafinsa na X.
1220 GMT — Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar lafiya
Duka asbitoci a arewacin Gaza sun daina aiki, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.
Ma’aikatar ta bayyana cewa a halin yanzu ana kokarin fitar da marasa lafiya da ke Asibitin Indonesia.
A bangare guda kuma ma’aikatar ta bayyana cewa akwai mutum 259 wadanda aka raunata, da farar hula da dama a cikin Asibitin Al Shifa kuma babu ranar kwashe su.
0920 GMT — Hezbollah ta dauki nauyin kai wani hari kan Isra'ila
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta dauki nauyin wani hari da aka kai kan wasu gidajen da sojojin Isra’ila ke zama a Metulla da ke arewacin Isra’ila.
Hezbollah ta bayyana cewa ta kai wannan harin ne domin ramuwar gayya kan gidajen kai iyaka da Isra’ilar ta kai wa hari a kudancin Lebanon.
A ‘yan kwanakin nan, Hezbollah ta kara yawan hare-haren da take kaiwa kan sojojin Isra’ila a kan iyaka, inda take kai hare-hare kusan goma a rana.
0715 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa 20 a sansanin 'yan gudun hijira
Akalla Falasdinawa 20 Isra'ila ta kara kashewa a hare-haren da ta kai gidaje biyu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza ta bayyana.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ilar ke ci gaba da kai hare-hare kan gidaje da asibitoci a Gaza.
Zuwa yanzu akalla mutum 13,000 Isra'ilar ta kashe wadanda akasarinsu yara ne kanana da mata.
0640 GMT — Isra'ila ta rusa masallatai 83 a Falasdinu
Akalla masallatai 83 Isra’ila ta rusa baki daya a hare-haren da take kaiwa cikin Falasdinu tun daga 7 ga watan Oktoba, inda ta kuma lalata 170, kamar yadda kafar watsa labarai ta gwamnatin Gaza ta bayyana.
Falasdinawa sun zargi Isra’ila da kai hari masallatai a Gaza da gangan domin lalata su.
Sai dai a nata bangaren Isra’ilar ta zargi dakarun na Hamas da amfani da masallatai a matsayin mafaka don guje wa hare-harensu.
0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a Gaza
Shugaban Hamas Isma'il Haniyeh ya ce ƙungiyar gwagwarmayarsa na gab da cimma yarjejeniyar sulhu da Isra'ila, a cewar wata sanarwa da aka wallafa ta kafar Telegram.
"Ana gab da cimma yarjejeniya kan sulhu," in ji Haniyeh, a cewar sanarwar
Masu shiga tsakani sun yi ta ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya don ba da damar sakin kusan fursunoni 240 da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, a lokacin harin da aka kai wa Isra'ila mafi muni a tarihinta.
Mayakan Hamas sun kuma kashe mutum kusan 1,200 a harin da suka kai kan iyaka.
Isra'ila ta kaddamar da hare-haren bama-bamai ba tare da bata lokaci ba tare da kai farmaki ta kasa a matsayin ramuwar gayya kan harin, inda ta lashi takobin rusa Hamas tare da ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
0117 GMT — Jami'in WHO ya ce halin da asibitin Gaza ke ciki ya zama 'bala'i'
Wani babban jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya bayyana halin da ake ciki a asibiti a Gaza a matsayin "mummunan bala'i", yana mai cewa yawanci ba sa aiki kuma abin da ya rage zai iya durkushewa sakamakon dubban haihuwar da ake sa ran mata za su yi a wata mai zuwa.
Bayanin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne sa'o'i kadan bayan da wani hari da aka kai ya shafi hawa na biyu na wani asibiti a arewacin Gaza, inda ya kashe mutum 12, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da kuma wani ma'aikacin lafiya.