Isra'ila ta ce ta ta kai hare-hare biyu waɗanda rundunar kare fararen-hula ta ce sun jikkata mutanen da dama. / Hoto: AA / Photo: Reuters

1328 GMT — Tawagar Isra'ila ta isa birnin Alkahira domin ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta

Tawagar Isra'ila ta isa Masar domin ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a daidai lokacin da Isra'ila da Hamas ke nazarin shawarar baya-bayan nan, in ji wasu jami'an filin jirgin saman Masar uku.

Tawagar Isra'ila ta hada da jami'ai shida, in ji jami'an filin jirgin ba tare da bayyana sunayensu ba.

Jami’an sun yi magana ne saboda ba su da izinin tattaunawa da manema labarai kan zuwan.

0908 GMT — Hezbollah ta sha alwashin kai hari kan sabbin wuraren Isra'ila saboda kashe fararen hula a Labanon

Ƙungiyar Hizbullah za ta ci gaba da kai hare-hare kan wasu sabbin wurare a kasar Isra'ila, idan har ta ci gaba da kashe fararen hula a kasar Labanon, in ji shugaban kungiyar Hassan Nasrallah, yana mai nuni da karuwar adadin wadanda ba mayaka ba da aka kashe a kasar ta Labanon cikin 'yan kwanakin nan.

Fararen hula biyar dukkansu ‘yan kasar Syria ne da suka hada da kananan yara uku aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a kasar Lebanon a ranar Talata, sannan a kalla fararen hula uku ne suka mutu kwana ɗaya kafin nan, kamar yadda kafafen yada labarai da jami’an tsaro suka bayyana.

"Ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula zai sa 'yan adawa su harba makamai masu linzami a matsugunan da ba a kai musu hari a baya ba," in ji Nasrallah, a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin na tunawa da ranar Ashoura.

0030 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare ta sama guda uku cikin ƙasa da awa ɗaya waɗanda suka kashe Falasɗinawa aƙalla 48 a Gaza, a cewar rundunar kare fararen-hula ta yankin.

Isra'ila ta ce ta ta kai hare-hare biyu waɗanda rundunar kare fararen-hula ta ce sun jikkata mutanen da dama.

Wasu sabbin alƙaluma da aka fitar sun nuna cewa mutum 25 sun mutu a makarantar Al Razi da ke cikin sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat na tsakiyar Gaza wadda ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda shugaban makarantar Mohammed al Mughair ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kazalika dakarun Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 18 sannan suka jikkata mutum 25 a harin da suka kai garin Al Mawasi da ke kusa da birnin Khan Younis na kudancin Gaza. Haka kuma sun kashe mutum biyar da ke tsaye a kusa da wani shatale-tale a garin Beit Lahia da ke Gaza, a cewar wasu jami'ai.

0140 GMT — Kafofin watsa labaran Lebanon sun ce yara uku na cikin mutum biyar da Isra'ila ta kashe a hare-hare ta sama

Kafofin watsa labaran Lebanon sun ce hare-haren da dama da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar sun yi sanadin mutuwar mutum biyar cikinsu har da yara uku 'yan ƙasar Syria, yayin da ƙungiyar Hezbollah ta sanar da harba rokoki kan Isra'ila a matsayin martani.

"Yara uku 'yan ƙasar Syria na cikin waɗanda maƙiya suka kashe" a harin da suka kai a wata gona a ƙauyen Umm Toot", a cear kamfanin dillancin abarai na National News Agency (NNA).

Ya ƙara da cewa jirgi mara matuƙi na "maƙiya" ta kai hari kan 'yan Syria guda biyu da ke tafiya a kan baburi a hanyar Kfar Tebnit da ke kudancin Lebanon.

Wata majiya a hukumar tsaron Lebanon wadda ba ta so a ambaci sunanta, ta shaida wa kamfanin dillancin labara na AFP cewar 'yan Syrian biyu da aka kashe "fararen-hula" da ke aiki a kusa da inda aka kai harin.

2324 GMT — Shugaban sojojin Isra'ila ya buƙaci Netanyahu ya nemi gafara daga wurinsu

Shugaban rundunar sojojin Isra'ila Herzi Halevi ya buƙaci Firaminista Benjamin Netanyahu ya nemi gafara daga gare su saboda sukar da ya yi wa sojoji a kwanakin baya cewa ba sa matsa lamba sosai kan masu fafutuka na ƙungiyar Hamas don samun ci gaba a tattaunawar neman sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Gidan talbjin na Channel 12 da ke Isra'ila ya ruwaito cewa a ranar Asabar Netanyahu ya ce "an kwashe watanni da dama ba tare da samun ci gaba ba, saboda sojoji ba sa matsa lamba sosai, kuma ina idan muna so a ƙulla yarjejeniya don sako mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan mu samu nasara a kan Hamas, dole mu shiga Rafah."

A lokacin wani taro da ya gudanar ranar Lahadi wanda kuma ya samu halartar shugabannin biyu daga cikin manyan hukumomin leƙen asirin Isra'ila, Shin Bet da Mossad, Halevi ya buƙaci Netanyahu ya nemi afuwa daga gare su, in ji Channel 12.

Halevi ya gaya wa Netanyahu cewa: "Waɗannan kalamai suka da kaushi. Ina buƙatar Firaminista ya nemi gafara."

Sai dai gidan talbijin ɗin ya ce Netanyahu bai nemi gafara ba.

TRT Afrika da abokan hulda