Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin shugaban ƙungiyar Hamas da ke fafutukar kare ƴancin Falasɗinawa Ismail Haniyeh a Istanbul inda suka tattauna kan hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kaiwa Gaza.
A ganawar da suka yi ranar Asabar, shugabannin sun tattauna kan matakan da suka kamata a ɗauka don tabbatar da kai kayan agaji Gaza ba tare da tarnaƙi ba, da kuma yadda za a samu dawwamammen zaman lafiya a yankin.
Erdogan ya jaddada cewa Ankara na ci gaba da aiki babu dare babu rana a fannin diflomasiyya domin jawo hankalin duniya game da gallazawar da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma buƙatar tsagaita wuta nan-take.
Da yake tsokaci game da jijiyoyin wuyan da ake tayarwa tsakanin Isra'ila da Iran, ya ce bai kamata hakan ya kawar da hankulan duniya game da ɓarnar da Isra'ila take tafkawa a Gaza ba.
Erdogan ya ce Turkiyya na yin dukkan abin da ya dace wajen kafa ƙasar Falasɗinu domin kuwa hakan ne kawai zai wanzar da zaman lafiya a yankin, yana mai shan alwashin tabbatar da ganin an hukunta Isra'ila kan kisan ƙare-dangi da take aikatawa.
Turkiyya na kan gaba a ƙasashen da ke kai kayan agaji Gaza inda kawo yanzu ta aika da tan dubu 45. Kazalika ƙasar ta aiwatar da takunkumai daban-daban da aka ƙaƙaba wa Isra'ila, ciki har da dakatar da cinikayya.