Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayar da umarnin ƙera jirage marasa matuƙa na yaƙi 'masu yawa', kamar yadda kafar watsa labarai ta ƙasar ta ruwaito a ranar Juma'a.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar yadda dangantakar ƙasar ke ƙara ƙarfi tsakaninta da Rasha ta ɓangaren soji ke ƙaruwa.
Kim a ranar Alhamis ya kai ziyara a lokacin da ake gwajin jiragen waɗanda aka ƙera su domin kai hari a cikin ruwa da kan tudu, wanda kamfanin ƙera jirage marasa matuƙa na Koriya ta Arewa ke ƙerawa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar KCNA ya ruwaito.
An tsara jiragen ne domin su yi jigilar ababen fashewa tare da jefa su kan abokan gaba.
A gwajin da aka gudanar a ranar Alhamis, an ga yadda jiragen marasa matuƙa suka kai hari "daidai saitin" da suka harba bama-baman.
Kim ya ƙara da cewa jiragen marasa matuƙa na da "sauƙin amfani... wurin kai hari" sakamakon sauƙin farashin ƙera su da kuma nisan zangon da suke da su, kamar yadda KCNA ya ruwaito.