Fafaroma Francis ya gana da Falasdinawan da 'yan uwansu ke maƙale a Gaza / Photo: Reuters

Takaddama ta barke kan ko Paparoma Francis ya yi amfani da kalmar "kisan kare dangi" wajen kwatanta halin da ake ciki a Gaza a wata ganawa da ya yi da Falasdinawa tun farko.

Iyalan Falasdinawa da 'yan uwansu wadanda ke tsare a gidajen yarin Isra'ila sun gana da Fafaroma a fadarsa ta Vatican a jiya Laraba

"Lokacin da muka ba da labarin iyalan da aka kashe (a Gaza da aka yi wa ƙawanya), ya ce, "Ina ganin kisan ƙare dangin," in ji Shireen Hilal a wani taron manema labarai bayan taron.

Ta ce Fafaroma yana da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a Gaza da suka hada da rashin samar da ababen more rayuwa da buƙatu kamar ruwa da wutar lantarki da magunguna.

Bayan tambayoyi da manema labarai suka yi kan ko Paparoma ya yi amfani da kalmar "kisan kare dangi," Hilal ta ce: "A bayyane yake cewa kalmar 'kisan kare dangi' ba ta fito daga gare mu ba, ta fito ne daga mai tsarki, Faparoma Francis.

Ta ce sun gayyaci Fafaroma zuwa Gaza, kuma ya ce hakan zai yi kyau kuma zai iya faruwa idan yanayi ya ba da dama.

A halin da ake ciki kuma, a wata rubutacciyar sanarwa, mai magana da yawun fadar Vatican Matteo Bruni, bai tabbatar da cewa Fafaroma Francis ya yi amfani da kalmar "kisan kare dangi ba.

"Ban san cewa ya yi amfani da irin wannan kalmar ba. Ya yi amfani da kalmomin da ya bayyana yayin taron jama'a da kuma kalmomin da a kowane hali ke wakiltar mummunan halin da ake ciki a Gaza," in ji shi.

Sauran iyalan Falasdinawa da suka halarci ganawar da Fafaroma kuma sun ce sun ji ya yi amfani da kalmar "kisan kare dangi."

Da yake amsa tambaya kan wannan batu a wani taron daban, Sakataren Harkokin Wajen Fadar Vatican Cardinal Pietro Parolin ya ce "kisan kare dangi" kalma ce ta fasaha da ta shafi taƙamaiman yanayi.

"Ban sani ba ko za mu iya magana kan kisan kiyashi a wannan lamarin,” in ji shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ANSA ya rawaito.

Da yake jawabi ga ɗaukacin mahalarta taron nasa, Fafaroma Francis ya ce ya yi ganawar daban da tawagogin Isra'ila da na Falasdinu

AA