Francis ya isar da sakon ne a wani taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Oslo. Hoto: Reuters

Shugaban mabiyar darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis ya yi gargadin cewa duniya na dab da fuskantar yakin nukiliya kamar irin rikicin makami mai linzami na Cuba na shekarar 1962.

Francis ya isar da wannan sako ne a wani taron kasashen duniya da aka gudanar a birnin Oslo don tunawa da ranar cika shekaru 60 na Fafaroma John XXIII da ya yi fice wajen kare martabar darikar Katolika ''Pacem in Terris'' a ranar Talata.

Kafar watsa labarai ta Vatican ta rawaito sakon Francis, inda yake cewa taron na zuwa ne a daidai lokacin da "duniyarmu ke ci gaba da fuskantar yakin duniya na uku, ga kuma mummunan yanayin rikicin Ukraine a yanzu wanda ke nuna yiwuwar fadawa rikicin makaman nukiliya."

Fafaroman ya yi kwatance tsakanin yanayin da ake ciki a yanzu da rikicin makami mai linzami na Cuba na watan Oktoban shekarar 1962, yana mai jaddada yiwuwar sake fadawa bala'in yakin nukiliya da duniya ta fuskanta a baya.

Ya bukaci taron da ya mayar da hankali kan sashen darikar Katolika da ke magana kan ajiye makami da bin hanyoyin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Fafaroma ya ce " samun duniyar da ta tsira daga makamin nukiliya abu ne mai yiwuwa wanda kuma ya kamata."

Kazalika Francis ya yi waiwaye kan bayanansa na taron tunawa da ranar zaman lafiya ta Hiroshima a shekarar 2019, inda ya ce "amfani da makamashin atomic don yaki ba abu ne mai kyau ba, kamar yadda mallakar makamin nukiliya bai dace ba."

Game da ire-iren makamai da ake amfani da su a yanzu, Francis ya ce "ya kamata a yi amfani da su wajen samar da tsaro da kariya kawai ba wai ana amfani da su wajen kai hare-hare kan fararen hula ba."

TRT World