Ko da yake fadar ba ta yi karin bayani kan aihinin nau'in cutar dajin da ke damun Sarki Charles III  ba, ta tabbatar cewa cutar ba ta da alaka da kansar mafitsara./Hoto: AFP

An gano cewa Sarki Charles na Ingila yana fama da cutar kansa kuma an soma yi masa magani, a cewar wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar.

Sanarwar da Fadar ta fitar ranar Litinin ta bayyana cewa tun da farko an gudanar da gwaje-gwaje a kansa na cutar daji wadanda daga bisani suka nuna cewa ya kamu da cutar.

Ko da yake fadar ba ta yi karin bayani kan aihinin nau'in cutar dajin da ke damun basaraken ba, ta tabbatar cewa cutar ba ta da alaka da kansar mafitsara.

"Sarki yana matukar godiya ga likitocinsa wadanda suka dauki matakin gaggawa sakamakon ziyarar da ya kai asibiti kwanakin baya," in ji sanarwar.

"Yana cike da kwarin gwiwa game da maganin da ake yi masa kuma yana fatan komawa bakin aiki nan ba da jimawa ba.

"Mai Martaba ya zabi sanar da batun rashin lafiyarsa ne domin kauce wa shafi-fadi da kuma fatan ganin hakan zai fahimtar da mutanen duniya halin da masu fama da cutar daji suke ciki."

TRT Afrika da abokan hulda