Dubban mutane daga Sudan wadanda suka yi nasarar tsere wa yakin da ake ci gaba da gwabzawa a kasar sun tsinci kansu cikin cunkoso a sansanonin 'yan gudun hijira, inda suke fama da azabar zafi a rumfunan roba da kuma matsalar rashin samun kulawar kiwon lafiya.
Daya daga cikin su, Adam Bakht, wani dattijo, ya ce yana fama da wasu cututtuka kamar “ciwon suga da asma.”
Ya ce an yi masa allura ne kawai don rage radadin ciwon, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a wani sansani da ke yankin Adre mai iyaka da Darfur na Sudan da ya yi fama da munanan tashe-tashen hankula.
Sanye da farar jallabiya mai haske, Bakht na tsananin jiran samun kulawa tare da wasu 'yan gudun hijira kusan 200,000 a garin wadanda ke kokarin ganin sun rayu.
Sansanonin da ke ba su kulawa na fama da karancin kayayyaki kamar ma'aikatan kiwon lafiya da magunguna har da makewayi - a cikin asibitocin na wucin gadi.
Kazalika, a kowace rana daruruwan mutane suke kara zuwa wannan waje, wadanda suka tsare da kafa don guje wa rikicin da ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF da kuma wasu mayaka sa-kai da suka shiga cikin fafatawar.
Marasa lafiya su 300 a kowace rana
Sabbin ‘yan gudun hijirar da suka isa Adre na iya kubuta daga hare-haren yakin, amma ba da jimawa ba za su fahimci cewa har yanzu suna cikin hadari - ciki har da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ke janyo barna a sansanonin da tuni ke fama da karancin abinci da ruwan amfani mai tsafta, a cewar kungiyar agaji ta Doctors without Borders (MSF).
“Cutar zazzabin cizon sauro ta karu matuka a lokacin da aka shiga damina a kasar Chadi, kuma mutane na fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka da ake iya kamuwa da ita kamar kwalara,’’ a gargadin da MSF ta yi
"A halin yanzu akwai cututtuka da dama da ke yaduwa," a cewar Muzammil Said, mai shekaru 27 da ya nemi mafaka a kasar Chadi, kafin ya nemi aikin sa-kai don taimaka wa daya daga cikin asibitocin da ke aiki.
A kowace rana, suna karbar "majiyyata kusan 300" wadanda ke kwanciya a kan gadaje da aka ajiye su kan yashi, kusa da juna
Kananan kungiyoyin ba su da wani wuri ko kayan aikin da za su iya wadata "asibitin" : an dai kafa wata rumfa ce da aka yi ta da itatuwa da ganyensu inda ma'aikata ke shiga don tsabtace kayan aikinsu.
Suna amfanin da sauran akwatunan magungunan da suka rage daga gudunmawar kasashen duniya.
''Samar da magunguna babban kalubale ne saboda yana da tsada sosai. Muna bukatar taimako," Said ya shaida wa AFP.
Yara masu fama da yunwa
Mutuwar kananan yara ta karu matuka a sansanonin, inda yara da dama ‘yan kasa da shekaru biyar ke mutuwa sakamakon rashin abinci mai gina jiki, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Tun da aka fara yakin, akalla yara 500 ne suka mutu sakamakon yunwa a Sudan, inda hukumar samar da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa sama da mutane miliyan 20 na fuskantar matsananciyar yunwa.
"Mafi yawan majinyatanmu suna fama da zazzabin cizon sauro da ciwon ido da cututtukan numfashi da kuma rashin abinci mai gina jiki," a cewar wani likitan sa-kai Nour al-Sham ga AFP daga sansanin "Arewa" da ke Adre.
Mutanen da suka fito daga Darfur, yanki da ya yi fama da mummunar matsalar talauci da yaki, sun jima suna fama da rashin samun tsarin kiwon lafiya mai inganci.
Tun kafin a farawar rikicin Sudan na yanzu a watan Afrilu, yara 78,000 ‘yan kasa da shekara biyar ke mutuwa a kowace shekara “sakamakon cututtuka da za iya samar musu da magani, kamar zazzabin cizon sauro,” a cewar MDD.
Hadarin kamuwa da cuta yana karuwa idan babu ruwa mai tsafta, ‘mutane kan fara yin layi... ‘tun daga karfe 2 na safe” cikin yanayin karancin a wasu sansanonin, in ji MSF.
Kungiyoyin ba da agaji – sun yi hasashen fuskantar kalubalen tsaro da wasu matsalolin - sun ce masu ba da agaji daga kasashen sun ba da kashi daya cikin hudu na kudaden da suka yi alkawarin za su bayar sama da watanni hudu a yakin.
karin wasu 'yan gudun hijira da za su gudu
Tun kafin rikicin Sudan na yanzu, kasar Chadi ta karbi bakuncin dubun dubatan 'yan gudun hijira daga Kamaru da ke yankin kudu maso yammacin kasar da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kudancin kasar, a yanzu dai bukatun mutane ya yi ma ta yawa kuma lamarin na kara tabarbarewa
Ban da 'yan gudun hijirar Sudan 410,000 da suka tsere wa mummunan yakin da ya barke a Darfur a shekarar 2003.
Sabon rikicin Sudan ya koro 'yan gudun hijira sama da 382,000 zuwa kasar Chadi, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sannan fiye da mutane 200,000 ke yankin Adre.
Bisa hasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, akwai yiwuwar wasu Karin mutane 200,000 su tsallaka iyakar Sudan sakamokon rikicin kasar da ya ki karawa.