Mutane da dama ne suka fita zanga-zangar wadda aka kaddamar da ita a Dandalin Trocadero da ke birnin Paris. / Hoto: Reuters

An gudanar da zanga-zangar adawa da dokar shige da fice ta Faransa a birane daban-daban na kasar, inda babban birnin kasar ya kasance cibiyar zanga-zangar.

Zanga-zangar wadda aka kaddamar da ita a Dandalin Trocadero a Paris a ranar Lahadi, ta samu halartar ƴan kungiyar kwadago da ƴan majalisa daga bangaren masu ra’ayin gurguzu na La France Insoumise daga ciki har da Mathilde Panot da Thomas Portes da Rachel Keke.

Masu zanga-zangar suna ikirarin cewa dokar tana nuna “wariya” kan baƙi da kuma ƴan Faransa masu takardar zaman kasa biyu, inda suka bukaci a bai wa duk wani mazaunin kasar katin zama.

Sakamakon wannan zanga-zangar, an kulle tashoshin jiragen sama da dama.

Sophia Binet wadda ita ce sakatare Janar ta gamayyar kungiyar kwadago a kasar ta wallafa sako a shafin X inda ta ce jimlar mutum 150,000 sun yi tattaki a fadin duniya, daga ciki har da mutum 250,000 a Paris, domin nuna kiyayyarsu da wannan dokar.

Rahotanni daga kafar kafar watsa labarai ta Faransa sun nuna cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta sanar da cewa mutum 16,000 sun gudanar da zanga-zanga a Paris da kuma mutum 75,000 a kasar baki daya.

Dokar shige da fice, wadda aka amince da ita a majalisar a ranar 19 ga Disamba, 2023, ta ce za a rinka bayar da tallafin haya da alawus-alawus na iyalai ga ƴan kasar waje da ke zaune a ƙasar kan wasu sharuɗa na aiki.

According to the law, employed foreigners can benefit from rental support three months after arriving in France, while non-working individuals can avail themselves of rental support after five years.

Kamar yadda dokar ta bayyana, baƙi da ke aiki a kasar za su iya samun tallafin kudin haya ne kadai watanni uku bayan sun isa Faransa, sai kuma wadanda ba su aiki za su iya samu bayan shekara biyar.

TRT World