Turkiyya za ta ci gaba da huldar diflomasiyya da niyyar tilasta wa Isra'ila cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, in ji Erdogan. / Hoto: AA / Photo: AA Archive / Photo: Reuters

1532 GMT — Sama da mata masu juna biyu 150,000 na fuskantar hadarin lafiya a Gaza — MDD

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza yana barin dubban mata masu juna biyu na kokawa da mummunan yanayin tsafta da kuma hadarin lafiya, in ji hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA.

"Fiye da mata masu juna biyu 150,000 na fuskantar mummunan yanayi na tsafta da kuma hadurran lafiya a cikin yanayin ƙaura da kuma yaƙi," in ji UNRWA a cikin wata sanarwa.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa hoton wata yarinya sabuwar haihuwa a yankin da yaki ya daidaita.

"An haifi Habiba a cikin wani karamin tanti. Tana da sati biyu, kuma nauyinta bai wuce kilogiram biyu ba," in ji shi. "Babu wani yaro a duniya da ya isa ya sha wahala haka."

1500 GMT — Turkiyya za ta ci gaba da ƙoƙarin tsagaita wuta a Gaza — Erdogan

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya za ta ci gaba da huldar diflomasiyya da niyyar tilasta wa Isra'ila cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma samun amincewar kafa ƙasar Falasdinu.

Shugaban na Turkiyya yana magana ne a taron manema labarai da Firaministan Girka Mitsotakis a Ankara.

"Mun tattauna batun kisan kiyashi a Gaza, muna sa ran goyon bayan Girka zai dakatar da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi," a cewar Erdogan. "Ya kamata Ƙasashen Yammaci da al'ummomin duniya su fito da muryarsu kan wannan kisan ƙare dangi."

Erdogan ya ƙara da cewa, samar da ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta wacce ta dogara da dokokin shekarar 1967, tare da Birnin Ƙudus a matsayin babban birninta, ita ce babbar mafita.

0901 GMT — 'Tsarin lafiyar Gaza zai rushe nan da awanni kaɗan saboda rashin fetur'

Ma’aikatar lafiya na Falasdinawa a Gaza tace nan da ‘yan sa’o’i kadan tsarin kula da lafiya na yankin zai durƙushe, bayan yakin da ake yi ya hana shigar da man fetur yankin ta hanyar muhimman iyakoki.

“Babu inda za a je. Babu tsaro ba tare da tsagaita wuta ba," in ji UNRWA. / Hoto: AA

“’Yan sa’o’i ne suka rage mana kafin tsarin kula da lafiyar a Zirin Gaza ya durkushe, saboda babu man fetur din da ake bukata don kunna injin samar da wutar lantarki a asibitoci da motocin daukar marasa lafiya da motocin daukar ma’aikata,” a cewar Ma’aikatar Lafiya cikin wata sanarwa.

0727 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi

Akalla ma'aikatan kiwon lafiya 500 ne aka kashe tun farkon yakin da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana a daidai lokacin da ake bikin ranar ma’aikatan jinya ta duniya.

Ma’aikatar ta lafiya ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila sun kashe malaman jinya 138 a wannan yaƙi.

Sannan akwai wasu ma’aikatan lafiyan 1500 da aka jikkata da kuma kama 312.

0630 GMT Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan wurare uku na Hezbollah a kudancin Lebanon

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wurare uku na kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon.

“Jiragen sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren harba makamai masu linzami na Hezbollah a kauyukan Helta da Al-Hamam da kuma lalata ababen more rayuwa mallakar kungiyar a yankin Khraibeh.

Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Hezbollah ta ce ta kai hari da wasu sabbin makamai masu linzami a kan wani wurin ajiye sojojin Isra'ila a kusa da yankin Zabdine a cikin gonakin Shebaa na Lebanon da suka mamaye.

TRT Afrika da abokan hulda