"Ba a ji ɗuriyar Sayyed Hassan Nasrallah ba tun ranar Juma'a da maraice," a cewar majiyar, wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta saboda girman lamarin.

Hezbollah ta tabbatar da cewa Isra'ila ta kashe shugabanta Hassan Nasrallah a wani hari da ta kai masa ta sama.

Tun da farko Isra'ila ta yi iƙirarin kashe Hassan Nasrallah a harin da ta kai Beirut.

"Hassan Nasrallah ya mutu," in ji wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojojin Isra'ila Laftanar Kanar Nadav Shoshani ya wallafa a shafinsa na X.

Tun da farko, Isra'ila ta ce ta kai hari a hedkwatar ƙungiyar da kuma wuraren ajiye makamanta a babban birnin Lebanon, sannan kafofin watsa labaran Isra'ila da Amurka su ruwaito cewa an kai harin na ranar Juma'a da daddare ne da zummar kashe Nasrallah.

Sai dai wata majiya ta kusa da Hezbollah ta ce yana cikin "ƙoshin lafiya".

"Ba a ji ɗuriyar Sayyed Hassan Nasrallah ba tun ranar Juma'a da maraice," a cewar majiyar, wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta saboda girman lamarin. Sai dai majiyar ba ta tabbatar da kisan Nasrallah ba.

Idan aka tabbatar da mutuwar Nasrallah, hakan zai kasance babban koma-baya ga ƙungiyar da ke ƙasar Lebanon wadda ya jagoranta tun shekarar 1992.

Isra'ila ta ƙaddamar da jerin zafafan hare-hare a kudancin Beirut ranar Juma'a da daddare wanda shi ne mafi girma da ta kai a yankin da Hezbollah ta fi ƙarfi tun yaƙin da suka yi a shekarar 2006.

TRT World