"Ba a ji ɗuriyar Sayyed Hassan Nasrallah ba tun ranar Juma'a da maraice," a cewar majiyar, wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta saboda girman lamarin.

Hezbollah ta tabbatar da kisan shugabanta Hassan Nasrallah a wani hari da Isra'ila ta kai masa ta sama a Beirut.

Tun da farko Isra'ila ta yi iƙirarin kashe Hassan Nasrallah, matakin da ake kallo a matsayin babban koma-baya ga ƙungiyar Hezbollah da ke ƙasar Lebanon wadda ya jagoranta tun shekarar 1992.

"Hassan Nasrallah ya mutu," in ji wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojojin Isra'ila Laftanar Kanar Nadav Shoshani ya wallafa a shafinsa na X.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari na yankan-shakku ranar Juma'a a yayin da shugabannin Hezbollah leadership suke gudanar da taro a hedkwatarsu da ke Dahiyeh, a kudancin Beirut.

Nasrallah shi ne mutum mafi ƙarfin faɗa a ji da Isra'ila ta kashe a makonnin da ta kwashe tana kai hare-hare kan mayaƙan Hezbollah.

Isra'ila ta ƙaddamar da jerin zafafan hare-hare a kudancin Beirut ranar Juma'a da daddare wanda shi ne mafi girma da ta kai a yankin da Hezbollah ta fi ƙarfi tun yaƙin da suka yi a shekarar 2006.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Lebanon ta ce mutane shida sun mutu sannan mutum 91 sun jikkata a hare-haren na ranar Juma'a, waɗanda suka ruguza rukunan gidaje shida.

Isra'ila ta ce ta kashe Ali Karki, Kwamandan Hezbollah da ke Kudancin yankin, tare da ƙarin kwamandojin ƙungiyar a hare-haren.

TRT World