Shahararren mai tsaron gida Wojciech Szczesny, wanda ya taka leda a Arsenal da Juventus, wanda kuma ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa a makonnin baya,ya dawo taka leda a Barcelona.
Barcelona ta samu nasarar ɗauko sabon mai tsaron gida ne bayan da babban mai tsaron gidanta, Marc-Andre ter Stegen ya samu rauni a gwiwa, wanda zai hana shi buga wasa don yin jinya ta tsawon lokaci.
An yi wa Stegen, wanda Bajamushe ne tiyata, kuma ana tsoron ba zai dawo buga ƙwallo ba sai bayan watanni takwas, wato har lokacin ƙare kakar wasan bana.
Mai yada labarun wasanni, Fabrizio Romano ya ruwaito cewa a yanzu Barca ta bai wa Szczesny, wanda ɗan Poland ne mai shekaru 34, kwantiragin shekara guda.
Rahoton ya ce Szczesny zai je Siafaniya don yin gwajin lafiya cikin kwanaki masu zuwa, bayan ya amsa tayin da Barca ta yi masa.
Barcelona ta samu zarafin kawo sabon gola a yanzu duk da ba a buɗe kasuwar cinikayyar 'yan wasa ba har sai watan Janairu. Ta ɗauko ɗan wasan ne saboda ba shi da kwantiragi da wata ƙungiya, wanda shi ne babban dalilin da ya sa ta nemo shi.
Szczesny dai ƙwararren gola ne wanda ya yi aiki da Arsenal da Juventus a zamaninsa. Sannan ya buga wa ƙasarsa Poland wasa sau 84, ciki har da a gasar Euro 2024.