Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira da a kama hanyar diflomasiyya yayin da Isra'ila ke zafafa hare-hare a Lebanon, yana mai gargaɗin Hezbollah da Isral'ila su "daina musayar wuta".
Da yake bayyana sake ɓarkewar rikicin na baya-bayannan a Gabas ta Tsakiya da "lokaci mai tsada" babban jami'in na diflomasiyyar Amurka ya ce, zaɓin da ɓangarorin biyu za su yi shi ne zai tantance a kan wace hanya yankin yake tafiya a kai, da irin mummunan tasirin da hakan zai haifar ga mutanen yankin a yanzu da ma mai yiwuwa har zuwa wasu shekaru masu zuwa".
"Abu mafi muhimmanci da za a yi ta hanyar diflomasiyya shi ne da farko a yi kokarin daina harba wa juna makmamai daga kowane bangare, sai kuma a yi amfani da lokacin da za a samu na tsagaita wutar a ga ko za a iya cim ma yajejeniyar diflomasiyya mai fadi," kamar yadda Blinken ɗin ya shaida wa manema labarai a wajen wani taron manema labarai ranar Juma'a yayin da ake ci gaba da Babbban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York.
"Da alama bin hanyar diflomasiyya tana da wahala a yanzu, amma dai tana nan, sannan a ra'ayinmu dole ne a bi ta, kuma za mu ci gaba da yin aiki ba dare ba rana da duka bangarorin da abin ya shafa don mu roke su su kama wannan hanyar," a cewarsa.
Rashin kwanciyar hankali da rashin tsaro mafi girma
Ya jaddada cewa hanya daya ita ce diflomasiyya da kuma tsagaita wuta a kan iyakar Isra'ila da Lebanon, yayin da sauran hanyoyin za su kara rura wutar rikici ne kawai, da tashe-tashen hankula da shan wahala da kuma rashin kwanciyar hankali da rashin tsaro mafi girma.
Blinken ya kuma bayyana cewa Amurka za ta dauki kowane irin mataki don kare muradun Amurka a yankin.
Ya jaddada matsayar gwamnatin Biden cewa har yanzu Amurka na tattara bayanai dangane da harin sojojin Isra'ila na baya-bayannan a kudancin Beirut ranar Juma'a.
Tun ranar Litinin Isra'ila ke kai hare-hare Labenon, inda ta kashe fiye da mutun 700 ta kuma jikkata kusan 2,200, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana.
Ma'aikatar ta ce adadin mutanen da aka suka mutu tun daga Oktoban da ya wuce sun kai 1,540, ƙari a kan fiye da 77,000 da aka tilasta wa barin gidajensu daga kudanci da gabshin kasar.
An ci gaba da zaman tankiya tsakanin Isra'ila da Lebanon tun daga lokacin da aka fara yaƙin ƙare-dangi a Gaza a watan Oktoban bara. Hare-haren bama-baman Isra'ila na ba ƙaƙƙautawa sun kashe fiye da mutane 41,500, mafi yawancinsu mata da ƙananan yara har zuwa yau.