Juma'a, 27 ga Satumban 2024
1549 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce sun kai wani hari a hedkwatar kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon da ke yankin kudancin birnin Beirut.
Kakakin rundunar sojin kasar Daniel Hagari ya bayyana a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin cewa, "Dakarun soji sun kai wani mummunan hari a hedkwatar kungiyar ta'addanci ta Hezbullah da ke Dahiyeh."
Harin dai shi ne mafi girma da aka kai a kudancin birnin Beirut, kamar yadda majiyoyin tsaro a kasar suka bayyana.
1130 GMT — Saudiyya ta sanar da ƙawancen ƙasashen duniya don matsa lambar bai wa Falasdinu cikakken 'yanci
Saudiyya ta sanar da kafa ƙawancen ƙasashen duniya da nufin samar da kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan a taron ministoci na ranar Alhamis kan batun Falasdinu da kokarin samar da zaman lafiya, ya bayyana cewa, "A yau, a madadin ƙasashen Larabawa da na Musulmi, tare da ƙawayenmu na Turai, muna sanar da ƙaddamar da ƙawancen ƙasashen duniya don aiwatar da shawarwarin samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, muna gayyatar ku da ku shiga wannan shiri."
Da yake magana a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, bai bayar da wani karin bayani kan ƙawancen ba, amma ya bayyana hakan ne saboda nuna yunkurin kasashen duniya.
Faisal ya yi tir da "mummunan rikicin jinƙai" da Tel Aviv ta haifar a Gaza da kuma "mummunan keta haddin da sojojin mamaya na Isra'ila suka yi a Gabar Yammacin Kogin Jordan", in ji kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA.
Ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin wani bangare na "tsarin siyasa na mamaya da kuma ta'addanci".
“Hakkin kariyar kai ba zai iya ba da hujjar kisan dubban fararen hula ba, inda ake halaka mutane a kullum da tilasta wa mutane yin gudun hijira da amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi da tunzura ƙiyayya da rusa ɗan'adam, ko amfani da azabtarwa gami da cin zarafinsu ta hanyar lalata da sauran laifukan da aka rubuta bisa rahotannin Majalisar Dinkin Duniya," in ji shi.
0328 GMT — Isra'ila ta kai mummunan hari wata makaranta a Gaza wanda ya kashe mutum 11
Wani hari da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ta zama mafakar dubban Falasdinawan da suka rasa matsugunansu a arewacin Gaza ya kashe akalla mutane 11 tare da raunata 22, ciki har da mata da yara, in ji Ma’aikatar Lafiya ta yankin.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai hari a makarantar da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia.
Hotunan makarantar Al Falouja sun nuna yadda jami'an ceto suke ta gudu ɗauke da wadanda suka jikkata daga harabar makarantar suna kutsawa cikin tarkace da cunkoson jama'a don ceton su.
Wani bidiyo ya nuna wasu mazaje suna naɗe wata gawa da ta yi rugu-rugu, suna kuma sanya sassan jikin mutane a cikin na'urar sanyaya abu.
Karin bayani 👇
2050 GMT — Isra’ila ta kashe mutane 92 a sabon harin da ta kai a Lebanon
Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, Isra'ila ta kashe mutum 92 a hare-haren da ta kai a wasu yankuna na kasar Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
A jerin bayanan da ta fitar, ma'aikatar ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 40 a garuruwa da kauyukan da ke kudu, 48 a yankuna biyu na gabashi da hudu a gabashin tsakiyar tsaunin Lebanon.
Gabaɗaya, ya ce mutum 153 sun sami raunuka. A halin da ake ciki, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa a fadin kasar ya kai 1,540 tun daga watan Oktoban bara.
0152 GMT — Kuwait ta yi kashedi kan 'mummunan tashin hankali' a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Lebanon
Kuwait ta ƙara nuna damuwa game da "mummunan ci gaba" da hare-haren Isra'ila ke kaiwa Labanon, tare da jaddada bukatar yin "hukunce-hukuncen siyasa na gaske na yin garambawul ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin kawar da rashin zaman lafiya a duniya."
Yarima Mai Jiran Gado na Kuwait Sheikh Mishal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York.
Yarima mai jiran gado Al-Sabah ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da kuma hare-haren soji kan kasar Labanon, lamarin da ya janyo asarar rayukan fararen hula da dama, yana mai bayyana ci gaba da ta'azzara da lamarin ke yi a matsayin keta dokokin ƙasa da ƙasa.
Ya kuma soki Isra'ila da keta hurumin ƙasar Labanon da yunƙurin janyo Lebanon cikin rikicin yankin.