Rikici ya ta'azzara yayin da China ta ƙaddamar da atisayen soji a kusa da iyakar Taiwan

Rikici ya ta'azzara yayin da China ta ƙaddamar da atisayen soji a kusa da iyakar Taiwan

Mashigar Teku ta Taiwan, wadda hanya ce mai muhimmanci ga safarar jiragen ruwa ta duniya, na ci gaba da zama matattarar soji.
Jirgin yakin China ya gifta ta kusa da Babban Jirgin Yakin na AMurka a mashigar tekun Taiwan. / Photo: Reuters

China ta kaddamar da atisayen jiragen sama na yaki a sararin samaniyar mashigar Tekun Taiwan a ranar Litinin, a wani bangare na atisayen soji da manufar aike wa da sakon "gargadi" ga tsibirin da ke jagorantar kansa.

Bari mu yi duba ga Mashigar Tekun mai muhimmanci da yadda take jan hankalin sojojin kasashe:

A ina Mashigar Tekun Taiwan take?

Mashigar tekun ta raba lardin Fujian dake kusu maso-gabashin China da Tsibirin Taiwan, yankin da ke da mutane kimanin miliyan 23.

A waje mafi kusanci da juna, ruwan teku da fadin kilomita 130 ya raba kasashen biyu, da ma wasu tsibiran Taiwan da dama da suka hada da Kinmen da Matsu - wadanda ke da tazarar 'yan kilomitoci daga gabar China.

China da Taiwan sun balle daga bayan da sojojin Mao Zedong suka yi nasarar yakin basasa tare da korar 'yan adawa zuwa mashigar a 1949,

Me ya sa yake da muhimmanci?

Mashigar tekun hanya ce mai muhimmanci ga safarar teku a duniya inda jirage da dama ke giftawa ta yankina kowacce rana.

Kimanin kayyaki da suka kai darajar dala tiriliyan 2.45 - sama da kashi biyar na kasuwancin duniya daka yi ta teku a 2022 ne ya gifta ta wannan yanki, kamar yadda Cibiyar Nazarin Kasuwanci ta Kasa da Kasa da ke Washington.

Taiwan na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin duniya - madalla da samar da sama da kashi 90 na maganadisun chip da ake amfani da shi a nau'ura mai kwalwalwa da manyan wayoyin hannu - da ma kayan ayyukan soji.

Masu nazari na cewa idan aka samu yaki na soji, za a yi illa babba ga samar da wadannan abubuwa.

Karin matsin lamba, kamar yi w ayankin kawanya, zai janyo sauya hanyoyin jiragen ruwa da soke tashin wasu wanda zai yi tasiri matuka ga masu saye da sayarwa a duniya.

Idan aka samu rikici mai tsayi da Taiwan, kasuwannin kudade za su hasala, kasuwanci zai ragu, kuma za a dakatar da jigilar kayayyaki ta teku, wanda zai jefa tattalin arzikin duniya cikin halin tsaka mai wuya," in ji Robert A. Manning, wani kwararre game da China da ke Cibiyar Stimson a Washington.

Wani rahoto da Rhodlum Group suka fitar ya yi hasashen cewa rufe hanoyin zuwa tsibirin zai janyo wa kamfanoni da suka dogara kan maganadisun chips din Taiwan asarar dala tiriliyan 1.6 a kowace shekara.

Me China ta yi shela?

Beijing ta bayyana cewa ta kaddamar da atisaye soji mai suna ""Hadin Kan Takubba-2024B" a yankunan arewavi, kudanci da gabashin Taiwan.

Dakarun sojin China sun aike da jiragen sama na yaki, jiragen haura bama-bamai da jiragen ruwa na yaki zuwa ga mashiigar, sannan sun gwada harba makamai masu linzami, inji kafar yada labarai ta kasar.

Sojojin sun kuma bayyana kai jirgin ruwa mai duakar jiragen sama na yaki, the Liaoning, don "don kai farmaki kan wurare a ruwa da tsandauri da ma sararin samaniyar gabas" a tsibirin.

Dakarun kan iyakar teku sun ce jiragen sama hudu na kewaye da sanya idanu a daura da tsibirin Taiwan, kuma ana gudanar da tattaki a kusa da Matsu.

Mahukuntan China sun bayyana cewa atisayen "na jarraba ayyukan hadin gwiwar dakarun fagen daga" inda ake kuma aike wa da gargadi ga 'yan awaren Taiwan da ke neman 'yancin kai.

Taiwan ta soki wadannan ayyuka na China d ata kira "mara amfani da takalar fada", kuma Amurka ma ta kira su da ba a bukatar su.

Wannan abu ya taɓa faruwa a baya?

A karshen watan Mayu, kwanaki uku bayan rantsar da Shugaba Lai Ching-te China ta kaddamar da Atisayen Hadin Gwiwaw Takubba na 2024A, mafarar atisayen da take yi a yanzu.

Sojojin China sun kuma yi atisaye a kewayen Taiwan a watan Afrilun bara, don mayar da martani ga shugabar da ta gabaci Lai, mai suna Tsai ing-wen, wadda ta gana da kakakin majalisar dokokin Amurka Kevin McCarthy.

A 2022, Beijing ta kaddamar da shawagi na tsawon makonni bayan Nancy Pelosi da ta maye gurbin McCarthy ta ziyarci Taiwan.

Rikici da dama da aka yi a shekarun baya,a tsakanin 1995 da 1996, a lokacin da China ta yi gwajin makamai masu linzami a kusa da Taiwan.

Har yanzu ba a gama tantance karfin atisayen na ranar Litinin da wadanda aka yi a baya ba.

TRT World