Gwamnatin Tarayyar Rasha da kuma wasu jami'an Rasha ba su da hannu a cikin waɗannan ayyukan ta kowace hanya, in ji sanarwar da ofishin jakadancin ƙasar a Nijeriya ya fitar./Hoto:OTHER

Ƙasar Rasha ta nesanta kanta daga duk wasu masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar da ake yi a Nijeriya kan tsadar rayuwa.

Tun bayan fara zanga-zangar ranar 1 ga watan Agustan nan ne aka dinga ganin gungun mutane a jihohi da dama a fadin ƙasar suna ɗaga tutar ƙasar Rasha a yayin tattakin.

Masu sharhi kan harkokin yau da kullum sun yi ta jan hankalin 'yan Nijeriya a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta cewa hakan illa ne ga dimokuradiyyar ƙasa mai cikakken 'yanci irin Nijeriya wadda take ƙarƙashin mulkin siyasa.

A sanarwar da ya fitar a yau Litinin, Ofishin Jakadancin Rasha da ke Nijeriya ya ce "mun lura da rahotannin da kafafen watsa labaran Nijeriya ke fitarwa da kuma yaɗuwar wasu hotuna da bidiyoyi a intanet da ke nuna masu zanga-zanga a arewacin ƙsar suna ɗaga tutocin Rasha suna kiran sunan Shugaba Vladimir Putin.

"Gwamnatin Tarayyar Rasha da kuma wasu jami'an Rasha ba su da hannu a cikin waɗannan ayyukan ta kowace hanya. Kamar kullum, muna jaddada cewa Rasha ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashen waje ciki har da Nijeriya," in ji sanarwar.

Rasha ta ƙara da cewa "wannan aniyar ta masu zanga-zangar ta ɗaga tutocin Rasha zaɓi ne na ɗaiɗaikun mutane, kuma ba sa nuna wani matsayi ko manufofin gwamnatin Rasha kan batun.

"Muna mutunta dimokuradiyyar Nijeriya kuma mun yi imanin cewa zanga-zangar lumana bisa ga dokar Nijeriya alama ce ta dimokradiyya. Duk da haka, idan waɗannan abubuwan sun haifar da duk wani rikici ko tashin hankali za mu yi Allah wadai da su."

Rundunar sojin Nijeriya ta yi gargaɗi

A hannu guda kuma, Babban Hafsan Rundunar Tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya ce masu ɗaga tutar Rasha sun aikata laifin cin amanar ƙasa.

Da yake magana bayan kammala taron tsaro na gaggawa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Aso Rock, Janar Musa ya sha alwashin cewa doka za ta kama duk masu yin wannan abu.

“Baya ga haka, dukkanmu mun ga inda aka dinga ɗaga tutocin kasashen waje a cikin ‘yancin Nijeriya, kuma hakan ba zai yiwu ba. Muna gargaɗi da kakkausar murya kuma Shugaban Ƙasa ya ce mu shaida muku cewa ba za mu amince da wani ya rinƙa ɗaga tutar wata ƙasa a cikin Nijeriya ba. Laifin cin amanar ƙasa ne, kar wanda ya amince a yi amfani da shi don cimma wata manufa," in ji Janar Musa.

“Har ila yau, batun juyin mulki, Nijeriya kasa ce mai cin gashin kanta, Nijeriya kasa ce mai bin tafarkin dimokuradiyya, dukkan hukumomin tsaro suna nan don kare dimokradiyya da tabbatar da cewa dimokradiyya ta ci gaba da wanzuwa. Ba za mu yarda wani ya dauki kowane irin mataki ba, bisa kowane irin dalili na son sauya gwamnati. Dimokradiyya ce matsayarmu kuma ita za mu ci gaba da karewa.

“Ga wadanda suke ɗaga tutoci kuma idan za ku ga da yawa daga cikinsu yara ne ake turawa yin hakan. Muna bibiyar wadanda ke daukar nauyinsu. Wadancan suna tura su ne kamar ƙudaje. Mun gano waɗannan wuraren kuma za mu dauki mataki mai tsanani a kan hakan."

TRT Afrika