Rahotanni sun ce an kama Mista Durov a hanyarsa ta zuwa Azerbaijan. / Hoto: Getty Images

Jami’an tsaro sun kama fitaccen mai kuɗin nan kuma mamallakin kamfanin Telegram Pavel Durov, kamar yadda kafofin watsa labaran Faransa suka ruwaito.

Kafofin watsa labaran TF1 TV da kuma BFM TV sun bayyana cewa an kama Mista Durov ne a filin jirgin Bourget da ke wajen Paris. Gidan talabijin na TF1 ya bayyana cewa Durov zai tafi ƙasar waje cikin jirginsa a ranar Asabar a lokacin da aka kama shi, kuma an kama shi bayan samun takardar sammaci domin gudanar da binciken wucin gadi a kansa.

Rahotanni sun ce an kama Mista Durov ne kan zargin rashin sa ido a kan manhajarsa ta Telegram sakamakon ana abubuwa haka nan sakaka da kuma aikata laifuka.

Kamfanin na Telegram bai mayar da martani nan take ba bayan buƙatar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya aika masa da ita.

Gidan talabijin na TF1 ɗin ya bayyana cewa Mista Durov na hanyarsa ta zuwa Azerbaijan a lokacin da aka kama shi.

Kamfanin Telegram wanda hedikwatarsa ke Dubai, Pavel Durov ne ya ƙirƙiro ta wanda shi haifaffen Rasha ne wanda ya bar ƙasar a 2014 bayan ya ƙi bin umarnin rufe shafukan ‘yan adawa a manhajarsa ta VK wadda ya sayar.

Mista Durov wanda mujallar Forbes ta yi hasashen arziƙinsa ya kai dala biliyan 15.5, ya ce wasu daga cikin gwamnati sun matsa masa, amma ya yanke shawarar ya kamata manhajar ta kasance ba ruwanta da siyasa.

Reuters