Gwamnatin Nijeriya ta ce dole a kiyaye lafiyar fararen-hula a yanayi na yaki,/Hoto: Shafin Facebook na Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta ce ya kamata a aiwatar da tsarin kasashe biyu na Falasdinawa da na Isra'ila masu cin gashin kansu don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin bangarorin biyu.

A wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Maitama Tuggar ya fitar ranar Asabar ya jaddada kira a yi gaggawar tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Falasdinawa.

"Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana jaddada kira a gaggauta tsagaita wuta sannan a koma kan teburin sulhu don ci gaba da neman mafita ta lumana da kuma aiwatar da tsarin kasashe biyu masu cin gashin kansu don warware wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa," in ji sanarwar.

Labari mai alaka: Takaitaccen tarihin yadda Isra'ila ta mamaye Falasdinu

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ya ce rikicin ya jefa mutanen da ba su da hannu a kansa cikin mawuyacin hali, yana mai kira ga Isra'ila ta bari a shiga da kayan agajin jinkai Gaza.

"Mata da kananan yara da sauran mutane masu rauni da ba su ji ba ba su gani ba su ne wadanda suka fi dandana kudarsu sakamakon wannan rikici na kan mai-uwa-da-wabi.

"Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana kira ga gwamnatin Isra'ila ta bari a shiga da kayan jinkai ga miliyoyin mutanen da aka raba da muhallansu tun da aka soma rikicin. Rashin ruwa da abinci da magunguna da fetur ya ta'azzara mawuyacin halin da ake ciki a Gaza," in ji sanarwar.

Ya ce dole ne bangarorin biyu su kiyaye 'yancin dan'adam da dokokin jinkai na kasashen duniya wadanda suka bukaci a kare lafiyar fararen-hula a yayin da ake rikici.

"Gwamnatin Nijeriya tana goyon baya da kuma jaddada kira da a gaggauta samun tsari mai dorewa na jinkai tsakanin dakarun Isra'ila da Hamas a Gaza kuma tana neman a bude hanyar jinkai."

TRT Afrika