"A kullum sai mun gano sabbin kaburburan tarin mutane," cewar shugaban Hamas da yake magana kan "dubban shahidai da baraguzan gini ya rufe". / Hoto: AA

Shugaban Reshen Siyasa na ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh ya yi gargaɗi kan yiwuwar mamayar soji daga sojojin Isra'ila a Rafah, kuma ya ce haka zai iya haifar da kisan kiyashi kan Falasɗinawa.

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ranar Asabar, Haniyeh ya ce, “Ina kira da duka ƙasashe ƙawayenmu, da 'yan'uwanmu a Masar, da 'yan'uwanmu a Turkiyya, da 'yan'uwanmu a Qatar a matsayin masu shiga-tsakani, da ƙasashen Turai da su ɗauki matakin hana zaluncin (Isra'ila), don dakatar da hari kan Rafah, da kuma ficewar (sojin Isra'ila) gaba ɗaya daga Zirin Gaza da kawo ƙarshen hare-hare kan Gaza".

Game da fafutukar Falasɗinawa, Haniyeh ya ce, "Idan maƙiyanmu 'yan aƙidar Zionism suka shiga Rafah, al'ummar Falasɗinu ba za su zaɓi ajiye makami ba. Mayaƙanmu a Rafah sun shirya kare kansu da tirjiya ga azzalumai.”

Abin da Isra'ila take so 'haramtacce' ne

Da yake jaddada yadda Isra'ila ta ƙi amincewa da tsagaita wuta a Gaza duk da yawan tattaunawa da aka yi, bayan gabatar da gomman shawarwari ta hanyar masu shiga tsakani, Haniyeh ya ce: "Ba abin da take so sai ta karɓo fursunoninta sannan ta sake fara wani yaƙin a Gaza, kuma wannan ba zai yiwu ba."

"Dole sojin Isra'ila su fice daga Gaza gaba ɗaya. Isra'ila ba ta ƙaunar ganin mutanen da suka bar arewacin Gaza sun koma gida. Tana amincewa ne da taƙaita masu dawowar a hankali. Wannan ba abin amincewa ba ne.”

Ya jadddada cewa Isra'ila ta gabatar da adadi kaɗan na mutane don yin musayar fursunoni duk, da cewa ta kame kusan Falasɗinawa 14,000 daga Gaɓar Yamma da kuma Gaza tun bayan 7 ga Oktoba.

Ya ƙara da cewa, “Isra'ila da Amurka ce, wadda ba ta wani matsin lamba (kan Isra'ila), kuma cewa tana hana cim ma wata yarjejeniya. Da zarar Isra'ila ta amsa buƙatunmu, a shirye muke mu cim ma yarjejeniya".

Haniyeh ya yi nuni da cewa yayin da Hamas ke nuna sauƙaƙawa a tattaunawa, Isra'ila ta doge kan tsattsauran matsayi, inda ya ɗora alhakin gaza cim ma matsaya kan wannan hali na Isra'ila.

Jagorancin Gaza bayan yaƙi

Haniyeh ya ambata cewa Gaza za ta zama ƙarƙashin jagorancin alasɗinawa bayan yaƙi ya zo ƙarshe.

Ya ce, “Hamas ba te cewa dole sai ta zama jagora tilo a Gaza, amma muna cikin Falasɗnawa kuma za mu iya kafa gwamnatin haɗin-kan ƙasa bisa doron haɗn gwiwa, sannan mu ci gaba da jagorancin Gaza".

"Wannan batutuwa ne na ƙasa. ba za mu bari batun Falasɗinawa a Gaza, da Gaɓar Yamma, ko duka biyun ya zama ƙarƙashin jagorancin 'yan mamaya ba ko wani daban”.

Haniyeh ya ce an ba da shawarwarin sauran zaɓin da aka da shi game da batun shugabancin Gaza, amma babu nasara tattare da wani zaɓi na daban.

"Mun yi kira na matakai biyu don kula da siyasar cikin gida ta Falasɗinu. Matakin farko ya haɗa da sake tsara ƙungiyar PLO don ta ƙunshi duka ƙungiyoyin Falasɗinawa.

"Na biyu shi ne kafa gwamnatin haɗin-kan ƙasa wadda za ta ɗauki alhakin sake gina Gaza da haɗa kan cibiyoyin da ke Gaɓar Yamma da na Gaza ƙaƙashin inuwa ɗaya, da kuma tabbatar da gabatar da zaɓen shugaban ƙasa, da na 'yan majalisu, da kafa hukumar zaɓe ta ƙasa".

Haniyeh ya janyo hankali kan cewa Gaza wani ɓangare ne na Falasɗinu, inda ya yi nuni da cewa Hamas tana sa ran samun gwamnatin ƙasa da kowa ya aminta da ita, wada za ta haɗe Gaza da Gaɓar Yamma ƙarƙashin jagoranci bayan yaƙi.

'Dubbar shahidai ƙarƙashin baraguzai'

Haniyeh ya ce Isra'ila, wadda ta yi luguden wuta kan Gaza daga sama kafin ta shigo daga ƙasa, ta zaɓi tsarin yin kisa, sannan ta fito da tsarin takunkumin soji da na kai kayan agaji, wanda ya lahanta asibitoci, da makarantu, da kayan more rayuwa, da gidajen biredi, da shagunan magani, da masana'antu.

Ya ce, "Cikin sama da watanni biyar, ba abin da ya shiga Gaza. An yi amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi, don karya gwiwar mutane da tilasta musu ƙauracewa zuwa kudu ko arewa. Yana da wahala ga yawan shahidai da kuma waɗanda aka jikkata, da waɗanda baraguzai ya rufe. Akwai "dubban shahidai da baraguzan gini ya rufe. A kullum sai mun gano sabbin kaburburan tarin mutane."

Netanyahu 'ba ya son kawo ƙarshen yaƙi a Gaza'

Dangane da tashintashina tsakanin Iran da Isra'ila, Haniyeh ya ce: "Duka wanna na nuni da abu biyu. Netanyahu 'ba ya son kawo ƙarshen yaƙi a Gaza. Saɓanin haka, yan so ya ƙara faɗin yaƙin a yankinmu. Haka nan, suna so Amurka ta shiga fagen yaƙin kan Iran, don zama wani ɓangare na sojin Isra'ila."

Ya ce, "Maƙiya 'yan aƙidar Zionist su ke da alhakin tashintashinar yankinmu, wadda ke hana mutane 'yancinsu, da cigaba da harin mutanenmu, da wuraren ibadarmu, musamman Birnin Ƙudus da masallacin al-Aqsa, sannan suna cigaba da yaƙin ƙare-dangi a Gaza."

‘Isra'ila na ƙaddamar da shingen 'yan jarida'

Da yake duba matsayar 'yan jarida kan Gaza, Haniyeh ya ce akwai kyakkyawan lura kan abin da ke faruwa a Gaza daga gidajen jaridar Turkiyya, da na Larabawa, da na sauran duniya.

Ya ƙarfafa cewa Isra'ila tana hana fitar labarai kuma tana hana ;yan jaridun duniya daga shiga yankin don daƙile bayyanar laifukanta da zaluncinta ga idanun duniya.

Haniyeh ya roƙi 'yan jaridar Turkiyya da sauran kafofi sun ci gaba da bankaɗo laifukan Isra'ila, da nuna salo-salon bala'in da ke faruwa a Gaza, don karya takunkumin jarida da Isra'ila ke sakawa.

Bayan ganawarsa da shugaba Recep Erdogan a Istanbul, ya faɗa wa Anadolu cewa wannan shi ne karonsa na farko da ya yi magana da gidan jaridar duniya tun bayan 7 ga watan Oktoba.

'Jinin 'ya'yana bai fi na 'ya'yan Falasɗinawa daraja ba'

Haniyeh ya yi nuni kan harin da ya kashe 'ya'yansa da jikokinsa, inda ya ce batun ya fito da abubuwa uku: "Na farko, gazawar maƙiya na cimma manufofin soji cikin watannin bakwai, baicin kashe farar hula, da dubban yara, da mata, da tsaffi. Don haka, kisan kiyashin da aka yi lokacin bukukuwan Sallah, inda aka kashe min 'ya'ya uku da jikoki biyar, shi ma yana nuna wannan batu da kuma gazawa maƙiya.

“Batu na biyu shi ne rashin fahimtar cewa don kisan ya shafi gidana, da 'ya'yana, da jikokina, wai hakan zai matsa wa shugabanci da ƙungiyarmu don ta yi sassauci a tattaunawar da ake yi, hakan yaudarar kai ne".

Ya ƙara da cewa, "Na uku, 'ya'yana wani ɓangare ne na al'ummar Falasɗinawa, kuma batunsu daidai yake da na mutanen Falasɗinu. Tun daga farkon fari, na ce jinin 'ya'yana bai fi na sauran 'ya'yan al'ummar Falasɗinu a Gaza da Gaɓar Yamma ko wani waje daraja ba”.

Haniyeh ya ƙara da cewa duka shahidai a Gaza, da Gaɓar Yamma, ko a waje, 'ya'yansa ne.

Ya ce, "Don haka, daidai muke a hakƙi, da kishin-kai, da sadaukarwa. Mun amince da wannan tare da cikakkiyar gamsuwa, da juriya da sadaukarwa. Ko me za mu rasa, kuma ko me ake buƙatar mu bayar, za mu ci gaba kan wannan bigire".

TRT World