1743 GMT — Ministan Ma'aikatar yaƙi ta Isra'ila Benny Gantz ya sauka daga muƙaminsa
Ministan Ma'aikatar yaƙi ta Isra'ila Benny Gantz ya sauka daga muƙaminsa tare da ficea daga gwamnatin-gaggawa ga Firaminista Benjamin Netanyahu a yayin da suka kwashe watanni takwas suna luguden wuta a Gaza.
"Muna cike da baƙin-cikin ficewa daga gwamnatin haɗin-kai," in ji Gantz a wani jawabi da ya gabatar a gidan talbijin.
Kazalika Gantz ya yi kira ga Benjamin Netanyahu ya gudanar da zaɓe "nan ba da jimawa ba".
Gantz, wanda tsohon soja ne, ya shiga gwamnatin Netanyahu jim kaɗan bayan harin ba-zata da ƙungiyar Hamas ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
1458 GMT — Wani asibitin Gaza ya samu yara 50 da ke fama da rashin isashen abinci
Wani asibiti a arewacin Gaza ya ce a cikin mako daya kacal ya samu yara 50 Falasɗinawa waɗanda ke fama da rashin isashen abinci.
Hossam Abu Safiya wanda shi ne daraktan Asibitin Kamal Adwan, shi ya bayar da rahoton waɗannan alƙaluma a wata sanarwa da ya fitar.
“Ɓangaren lafiya na Gaza ya kasance wurin da Isra’ila ke hari, amma muna ƙoƙarin ci gaba da aikin samar da lafiya a ko yaya ne saboda ƙarancin fetur,” kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana cewa "yanayin bala'i ne," yana mai jaddada cewa "yunwa na neman mamaye Gaza."
Sakamakon yakin da ake ci gaba da yi da kuma takunkumin da Isra'ila ta saka, akwai ƙarancin abinci, ruwa, magani, da man fetur a Gaza.
1041 GMT — Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a sansanin Nuseirat ya kai 274
A yayin da ake ci gaba da jimami a Gaza, adadin Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe a sansanin gudun hijira na Nuseirat ya ƙaru zuwa 274, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta tabbatar.
A ranar Asabar ne da safe Isra’ila ta kai hari sansanin, inda alƙaluma na baya-bayan nan da ma’aikatar lafiyar ta sanar suka nuna cewa mutum 698 ne suka jikkata.
Ƙasashen duniya da ƙungiyoyi sun ta yin Allah wadai da wannan kisan na baya-bayan nan da sojojin Isra’ila suka aikata.
1011 GMT — Kai-tsaye: MDD ta nuna damuwa kan harin Isra'ila da ya kashe sama da mutum 200 a rana guda
Shugaba Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna damuwarsa dangane da irin harin da Isra’ila ta kai a sansanin gudun hijira na Nuseirat wanda ke a tsakiyar Gaza, wanda ya ja aƙalla mutum 210 suka rasu sannan sama da 400 suka jikkata.
“A yau, sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat shi ne cibiyar bala'i da farar hular Gaza ke ci gaba da fuskanta,” in ji shi.
Hotunan irin yadda aka samu mace-mace bayan harin Isra’ila na ƙara nuna hujjar cewa Isra’ila na ci gaba da yaƙin nan a kullu, kamar yadda Martin Griffiths ya bayyana a wata sanarwa.
Griffiths ya sake nanata cewa babu inda ke da aminci a Gaza kuma kula da lafiya a yankin da aka yi wa kawanya "na cikin mawuyacin hali."