Fidan and Haniyeh sun tattauna kan batun tsagaita wuta nan-take a Gaza da kara kai kayan agaji yankin da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da kasashe biyu masu 'yancin kansu./Hoto: OTHER

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, a cewar wasu majiyoyi na diflomasiyyar Turkiyya.

Fidan and Haniyeh sun tattauna ranar Asabar kan batun tsagaita wuta nan-take a Gaza da kai karin kayan agaji yankin da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da kasashe biyu masu 'yancin kansu.

Hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaza sun raba kashi 85 na mutanen yankin da muhallansu a yayin da ake cikin tsananin rashin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna, sannan an rusa kashi 60 na gine-ginen yankin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A watan Oktoban da ya wuce, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Haniyeh bayan Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza inda ya tabbatar masa cewa Ankara zai kai kayan agaji Gaza sannan za a dauko wadanda suka jikkata a yankin domin kawo su Turkiyya su yi jinya idan akwai bukatar hakan.

Shugaba Erdogan ya jaddada cewa ba za a samu dauwamammen zaman lafiya a yankin ba sai Falasdinawa sun samu kasa mai zaman kanta kamar yadda take a 1967 wacce Birnin Kudus zai zama babban birninta.

Erdogan ya kara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da fafutuka domin ganin an samu zaman lafiya a yankin.

Isra'ila ta kaddamar da hare-hare babu kakkautawa ta sama da ta kasa a Gaza tun bayan da Hamas ta kai mata barin ba-zata, wanda Tel Aviv ya ce ya kashe akalla mutum 1,200.

Ta kashe Falasdinawa akalla 24,927, galibinsu mata da kananan yara, sannan an jikkata mutum 62,388, a cewar hukumar lafiya ta Falasdinu.

AA