Shugaban Rasha Vladimir Putin na magana a wajen taron zaben sa a fadar Cremlin da ke Mosow. Rasha 20, Maris 2024. / Hoto: Reuters

Daga Hannan Hussain

A yanzu da Vladmir Putin ya sake lashe zaɓe a matsayin shugaban ƙasar Rasha, a bayyane take ƙarara cewa za a ci gaba da tashin-tashina tsakanin ƙasar da ƙasashen Yamma - kuma lamarin ma na iya ƙara munana.

A wannan makon, Moscow ta bi sahun China wajen amfani da ƙarfin ikonta a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya kan maslahar da ke kira ga - "wajabcin tsagaita wuta mai ɗorewa" a Gaza.

Jakadan Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya Vasily Nebenz ya ɗora laifi kan Amurka wadda ta kawo batun ƙudirin na tsagaita wutar da taƙe wasan siyasa da shi "da gangan don ɓatar da ƙasashen duniya".

A wata tattaunawa da aka yi da Putin kwanan baya, ya yi gargaɗi cewa Rasha ta shirya amfani da makaman nukiliya idan har aka yi wa ƴancin mulkinta barazana, yana mai cewa makamansu na nukiliya na cikin shirin yaƙi a koyaushe.

Waɗannan ƴan misalai ne na yadda rikici ka kara rincaɓewa tsakanin ƙasashen Yamma da Moscow.

Bayaga Gaza, akwai kuma rikicin Ukraine, ɗaya daga cikin manyan matsaloli. A makon jiya, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi barazanar aikawa da sojoji zuwa Ukraine don taimaka wa ƙasar. Amma yaƙi kai-tsaye tsakanin Rasha da NATO, na nufin mataki ɗaya zuwa ga "fara yaƙin duniya na III", in ji Putin yayin bayar da gargaɗi.

A gefe guda kuma, Firaministan Jamus Olaf Schol a baya-bayan nan ya faɗa wa ƙaramar majalisar dokokin ƙasar cewa Berlin ba za ta amince da "zaman lafiyar dole" da Putin ke bayyanawa ba game da Ukraine.

Tarayyar Turai kuma ta yarda ta ƙaƙaba sabbin takunkumai kan jami'an gwamnatin Rasha da wasu ƙungiyoyi saboda mutuwar babban abokin hamayyar Putin Alexei Navalny. Kuma masu goyon bayan shugaban rundunar sojin Ukraine na Yammacin duniyana yin alƙawarin kai makamai.

Hoton da aka dauka ranar 22 ga Maris 2024 na nuna gobara ta kama a karamar tashar rarraba lantarki bayan harin makami mai linzami a Kharkiv. (SERGEY BOBOK / AFP).

Amma Putin ya ceya ƙudiri aniyar samun cikakkiyar nasara a Ukraine, kuma ya yi alkawarin ƙarfafa ƙarfin ikon sojin Rasha. Ya kuma bayar da umarni ga Jami'an Tsaron Tarayya kan su taimakawa kamfanonin Rasha wajen ƙalubalantar takunkuman ƙasashen Yamma.

Zango na biyar na mulki zai iya bai wa Putin isasshiyar damar cim ma manufofin tattalin arziki da siyasa wajen ɗabbaka manufofinsa, musamman ma a yaƙin da ake yi Ukraine.

Putin na sa ran fadada karfin ikon Rasha a kan iyakoki sama da Ukraine, kuma yana shirin samar da wani yanki na kariya don hana afkuwar hari ta kan iyakoki. Duk wannan alamace ta cewa Putin ba zia ja da baya ba a yakin k ya bayar da kai bori ya hau ga kasashen Yamma ba.

Yammacin duniya ba shi da wasu zabi da yawa game da me za su yi kan Rasha. Bayan komai, ana smaun raguwar goyon bayan sojin Yammacin duniya ga Ukraine, kuma ana ganin yadda hakan ke zama marar farin jini.

Dakrun Ukraine a birnin Kiev yayin d aake tsaka da gwabza rikici da Rasha. (Genya SAVILOV / AFP).

Ministan Tsaron Ukraine Rustem Umerov ya ce alkawarurrukan Yammacin duniya na samar musu da makamai ba su tabbata ba, kuma sama da rabin makaman da aka turo ma ba su isa kasar ba.

Ko da goyon baya da taimakaon Yammacin duniya ya ragu soai, ba a da tabbacin har zuw aya8she ne za a su ci gaba da bayar da taimakon. Taimakon makamai a kai a kai bai agazawa ayyukan soji Ukraine a baya ba, kuma ana kallon ma ba za su iya kalubalantar hare-haren da za a kai musu ba.

Sabanin haka kuma, sabbin dabarun soji na Rasha a Ukraine na rikitar da kwakwalen kasashen Yamma: ko su ci gaba da yakin, ko su tankwara Kiev ta mika kai bori ya hau a nemi zaman lafiya.

Mataki na biyu na neman zaman lafiya ne abun da ya kamata a mayar da hankali a kai. Kasashen Yamma sun yi ta haushi game da yiyuwar tattaunawar zaman lafiya tsawon watanni, kuma suna kallon hakan kamar muka wuya ne ga Moscow. Amma wannan zai iya sauyawa duba da yadda Putin zai ci gaba da mulki har nan da 2030.

Duba ga Amurka: tana shirin gudanar da zabe wanda zai yanke hukunci game da matsayin Ukraine. Duk da shugaban Amurka Joe Biden ya zabi goya baya ga Ukraine, amma babban abokin hamayyarsa a zaben Nuwamba Donald Trump, babban mai adawa da yakin ne.

Trump na bayyana cewa zai iya kawo karshen yakin a cikin awnani 24, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen bayar da taimakon soji na biliyoyin daloli ga Kiev. A yayin da tauraruwar Trump ke haskawa, watakila Putin ya dan saurara ya ga yadda za ta kaya don matakin da zai yanke kan Ukraine.

Shugaba Trump a wancan lokacin da Putin yauin da suke gaisawa a wajen taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a Helsinki, Finlan a ranar 16 ga Yuli, 2018. (REUTERS/Leonhard Foeger).

A daya bangaren kuma, Jamus, Birtaniya da Faransa suna kara kidimewa kan yadda Moscow ke ci gaba da yaki a Ukraine.

Duk wani motsi na dakarun NATO a yankin, zai ta'azzara rikicin ne, kuma Putin ya yi gargadi ga Yammacin duniya kan keta wannan layi. Kawayen Amurka a Turai na fuskantar matsin lamba da su guji rikici na kai taye tsakanin Rasha da NATO.

Wani sabon rahoto da aka fitar ya bayyana cewa daga Cibiyar Nazar Kan Yake-Yake, Moscow ta riga ta fara shirin tunkarar babban yaki da NATO. A karkashin wadannan shirye-shirye har da kara karfin dakarun sojin Rasha.

Putin ya shirya sanya idanu wajen sabunta kokarin sojin kasarsa, ciki har da samar da sabbin rundunonin hadin gwiwa nan da karshen wannan shekarar. Sauyi kan hakan shi ne kawai Yammacin duniya su kauracewa duk wani yaki da janyo fito na fito tsakaninsu da Rasha, sannan su hana rikicin Ukraine ama wanda ba za a iya shawo kansa ba.

Amma ba a da dabarun kaucewa rikicin da yawa

Amfani da karya tattalin arzikin Rasha da kasashen Yamma ke yi na da iyaka. putin na ta kokarin habaka tattalin arzikin Moscow daga shekarar bara, wanda ya bijirewa dubunnan takunkuman kasashen yamma.

Tarayyar Turai ma ta fuskanci tarzoma kan kwacewa da aika kaso 90 na biliyoyin dalaolin kadarorin Rasha da aka sanya wa takunkumai. Ta kalli wannan a matsayin babban yunkurin taimakawa Ukraine da makamai. Amma ana sa ran Putin duakar matakin shari'a wanda zai hana Yammacin duniya aikat ahakan.

A gefe guda kuma, karuwar rikici tsakanin ta da Yamma ba zai hana Rasha ci gaba da rungumar China ba, babbar kawa da ke taimakon Rasha ta jure wa takunkumin Yammacin duniya. Putin ya shirya ziyartar Beijing a tafiyar farko da zai yi zuwa kasar waje bayan lashe zabe, kuma kasashen biyu sun kudiri niyyar habaka alakarsu ta makamashi d abunkasa tattalin arziki.

Yunkurin ganin an dakile Rasha da mayar da ita aniyar ware da ake ci gaba da yi na iya taimaka mata wajen sake kulla alaka da akwance da manyan kasashe masu karfin tattalin arziki. Wadannan sun hada da audiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, China da kawar Amurka India. Uku na karshe da ma mambobin BRICS ne, kungiyar kasashe masu tasowa da habakar tattalin arziki da ske da manufar takaita mamayar Amurka a duniya.

A takaice, zango na biyar na Putin zai jarrabba goyon bayan da Yammacin duniya ke baiwa Ukraine, zai tirsasa NATO su sauya matsaya kan Rasha, sannan zai sanya da wahala takunkuman tattalin arzikin Yammacin duniya su yi wani babban tasiri kan tattalin arzikin Rasha da ke kara kulla alaka da wasu kasashen daban.

Marubuci, Hannan Hussain, kwararre ne kan harkokin kasa da kasa kuma marubuci. Malami ne mai lambar Fulbright kan tsaron kasa da kasa a Jami'ar Maryland, kuma ya yi aikin bayar da shawara ga Cibiyar New Lines da ke Washington. AN buga ayyukan Hussain a Mujallar Carnegie Endowment da Express Tribune da ma New York Times.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika