Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters / Photo: Reuters Archive

0942 GMT — Mayaƙan Houthi na Yemen sun ce sun kai hare-hare a kudancin Isra’ila da kuma kan wani jirgin ruwan Amurka a Bahar Maliya.

“Dakarunmu na ruwa ba za su daina ba har sai Isra’ila ta dakatar da kai hari kan Zirin Gaza,” kamar yadda mai magana da yawun sojojin na Houthi Yahya Saree ya bayyana a wani jawabi da ya yi ta talabijin.

Saree ya yi iƙirarin cewa ƙungiyar ta ƙaddamar da hari wanda ya faɗa kan wasu muhimman wurare a Eilat da kudancin Isra’ila ta hanyar amfani da makamai masu linzami.

Ya kuma bayyana cewa sun koma kai hari ga jirigin ruwan Amurka da makami mai linzami da jirgi maras matuƙi.

0017 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa goma a wasu hare-hare ta sama da ta kai gidaje biyu a tsakiya Gaza.

Wata sanarwa da hukumomin Asibitin Al Awda suka fitar ta ce an kai gawawwaki huɗu da kuma mutane da dama da suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai ta sama a wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat.

Rundunar Tsaron fararen-hula ta Gaza ta aike da saƙo ta manhajar Telegram cewa an kashe Falasɗinawa shida sannan aka jikkata wasu da dama a wani luguden wuta da sojojin Isra'ila suka yi a gidansu da ke sansanin Bureij.

Kawo yanzu ba a san takamaimai adadin mutanen da aka kashe ba.

Saƙon ya ƙara da cewa tawagar rundunar tana ci gaba da aiki don zaƙulo mutanen da ɓaraguzai suka binne.

Ganau sun shaida wa Anadolu cewa jiragen ruwan yaƙin Isra'ila sun rusa gidaje biyu— gidan iyalan Gharab a sansanin Nuseirat da gidan iyalan Khalifa a sansanin Bureij.

2344 GMT — Bai halatta mahukunta a Washington su tsara yadda makomar Gaza za ta kasance ba: Fadar shugaban ƙasar Falasɗinu

Fadar shugaban ƙasar Falasɗinu ta ce bayanan sirrin da aka kwarmata da suka nuna tattaunawar da Washington ke yi da wasu ɓangarori da ba a bayyana sunayensu ba game da makomar Gaza “ba ta da wani halacci” sanan ta jaddada cewa “babban abin da aka mayar da hankali a kai yanzu shi ne daina yin luguden wuta a Gaza.”

Kakakin Fadar shugaban ƙasar Falasɗinu Nabil Abu Rudeina ya fitar da sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, WAFA, ya ambato shi yana cewa Isra'ila tana ci gaba da "aikata laifuka a kan Falasɗinawa da ƙasarsu, da karya dokokin duniya sakamakon makauniyar soyayya da goyon bayan da take samu daga gwamnatin Amurka, wadda ke ba ta taimakon kuɗi da kayan yaƙi."

Rudeina ya ce mamayar da Isra'ila ta yi wa Gaza da gaɓar Yammacin Kogin Jordan ba ta halatta ba, a yayin da yake mayar da martani kan kalaman Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya yi watsi da hukuncin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta duniya cewa mamayar da Isra'ila ke yi wa yankin ta karya doka.

TRT Afrika da abokan hulda