Daruruwan masu zanga-zanga sun kai hari ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza, inda suka haura cikinsa sannan suka banka masa wuta don nuna fushinsu game da kasar da ta bari aka kona Alkur'ani mai tsari.
Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Alhamis cewa babu ma'aikacin ofishin jakadancin da ya jikkata sakamakon lamarin kuma ta ki yin karin bayani kan harin.
Jami'an ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza ba su ce uffan ba kawo yanzu game da wannan hari, yayin da shi ma ofishin harkokin wajen Sweden ya yi gum da bakinsa.
Ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta yi Allah wadai da wannan aiki kuma a wata sanarwa da ta fitar ta ce gwamnatin Iraki ta bayar da umarni ga jami'an tsaro su yi bincike nan take da zummar kamowa da hukunta masu hannu a wannan batu.
Magoya bayan fitaccen Malamin nan na mazahabar Shi'a Muqtada Sadr ne suka gudanar da zanga-zanga ranar Alhamis domin bijire wa shirin sake kona Alkur'ani a Sweden, a cewar wasu sakonni da aka wallafa a shafin Telegram wadanda ake alakantawa mabiya malamin.
Neman sake kona Alkur'ani
Ranar Laraba kamfanin dillancin labaran Sweden TT ya rawaito cewa 'yan sandan Sweden sun sake bayar da izini na gudanar da taron jama'a a wajen ofishin jakadancin Iraki da ke Stockholm a yau Alhamis.
Izinin ya hada da bayar da damar kona Alkur'ani da tutar kasar Iraki, a cewar TT.
TT ya ce mutum biyu ne za su kona Alkur'ani, yana mai cewa daya daga cikinsu shi ne wanda ya kona littafin mai tsari a watan jiya a wajen wani masallaci da ke Stockholm.
Masu zanga-zanga sun rika cewa Allah ya "daukaka Alkur'ani."
Daga baya wasu bidiyoyi sun nuna hayaki ya na fitowa daga ginin ofishin jakadancin.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters bai iya tantance sahinhanci bidiyoyin ba.
Babu cikakken bayani kan ko akwai mutane a ofishin jakadancin lokacin da aka cinna masa wuta.
A watan jiya, Sadr ya yi kira a yi zanga-zangar kyamar Sweden sannan a kori jakadanta da ke Iraki bayan wani mai zafin kin Musulunci ya kona Alkur'ani a Stockholm.