Yariman Saudiyya mai jiran gado Yarima Mohammed bin Salman, a hagu, tare da Firaiministan Isra'ila Minister Benjamin Netanyahu. / Hoto: AP      

Daga Hannan Hussain

Kulla alakar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Isra'ila zai yi wahalar gaske a daidai lokacin da Isra'ila ke cigaba da yakar Falasdinawa a Gaza.

Lallai Saudiyya na sha'awar kulla wata yarjejeniyar tsaro da Amurka, amma ba tare da shigar dq yarjejeniyar cewa dole sai ta amince da Isra'ila ba. Amma duk da haka, Amurka na cigaba da kokarin sulhunta tsakanin kasashen biyu, inda take nanata cewa hakan zai kara samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Wannan yunkurin ya sa ake tambayar wace ce da riba, kuma wa ke da asara idan aka yi wannan sulhun. Lallai akwai abubuwan da ya kamata a lura da su.

Da farko, sulhun da za a ce Amurka ce ta shiga tsakani, zai kawo tsaiko a kokarin da kasar China ke yi na sulhunta tsakanin Saudiyya da Iran. A bara China ta shirya wata zama tsakanin Saudiyya da Iran, kuma tana kokarin sulhunta tsakanin ne tare da kokarin shiga cikin harkokin tattalin arzikin kasashen biyu.

Masu zanga-zanga, mafi yawancinsu 'yan Houthi suna daga fastotci domin nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Sanaa da ke Yemen a ranar 26 ga Afrilun 2024. Hoto: (REUTERS/Khaled Abdullah).

Sai dai dukkan kokarin biyu akwai masu riba, kuma akwai masu asara. A sulhun da China ke kokarin jagoranta, akwai bukatar Iran za ta daina ba 'yan Houthi na Yemen makamai. Houthi na da tarihin yawan kai farmaki a kan wuraren makamashin Saudiyya, kuma ba sa shiri da Isra'ila.

Wannan bukatar zai samu tsaiko daga bangaren Houthi, da sauran kungiyoyin da suke da alaka da Iran, musamman wadanda suka so su yi amfani da wannan damar ta alakar Isra'ila da Saudiyya domin zama 'yan hana ruwan gudu.

Maslaha mai wahala

A daidai lokacin da Isra'ila ke ragargaza Gaza, su kuma 'yan Houthi suna cigaba ne da kai hare-hare a kan kadarorin Isra'ila da ke yankin Jan Teku, sannan kuma tana kai hare-hare a kan duk wata kasa da ke ganin tana da alaka da Isra'ila.

Don haka, sulhun zai iya dawo da hare-haren Houthi kan Saudiyya, wanda hakan zai iya sanyaya gwiwar kasar China da bata yunkurinta.

China tana bukatar zaman lafiya a yankin na Larabawa domin samun kulla alakar kasuwancin makamashi da sauran kasuwanci da yankin, wanda ya kunshi kasuwancin man fetur da kuma yarjejeniyar amfani da kudin Yuan wajen hada-hadar makamashin.

Wani hoto da ke nuna kauyen al-Mughayyer bayan bakin Isra'ila sun farmaki kauyen wanda yake yankin West Bank a Gaza a ranar 17 ga Afrilun 2024. Hoto: (REUTERS/Mohammed Torokman).

Sulhu tsakanin Saudiyya da Isra'ila kadai ba zai kawo karshen rikice-rikicen da ya dabaibaye yankin ba.

Misali, da wahala Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare a Gaza, saboda yadda masu ra'ayin rikau na kasar suke kara matsa lamba. Sannan kuma akwai yiwuwar wani rikicin tsakanin Yahudawa 'yan kama wuri zauna da Falasdinawa a Falasdinu, wanda shi ma zai bude wani sabon rikicin a nan gaba.

A daya gefen kuma, gyara alakar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Isra'ila za ta sa ita kuma Iran ta kara kaimi wajen shirinta na hada makaman nukiliya, wanda wani kalubale ne ga Saudiyyar da ma Isra'ila. Wanda hakan na iya dawo da hannun agogo baya a kokarin China na kawo zaman lafiya a yankin.

A bangaren Amurka, samun sulhun zai rage yunkurin China na kutsawa cikin tattalin arzikin Saudiyya. Amurka na ta kokarin fafatawa da China wajen zuba jari a kasar, sannan tana kokarin bin tafarkin Chinar wajen shiga wasu muhimman bangarorin kasar, kamar harkokin tsaro.

A matsayinta na kawar Saudiyya a harkokin tsaro da wasu muhimman harkokin yau da kullum, Amurka na son shiga tsakanin tare da sanya yarjejeniyar rage harkokin kasuwancin China a kasar. Tuni an fara tattauna yiwuwar kara wa Saudiyya makamai daga Amurka, idan har ta amince ta rage harkokin sayan makamai da kasuwanci da China.

Wannan kuma ba karamin kalubale ba ne ga China, wadda ta kuduri aniyar fadada kasuwanci a kasar ta Saudiy nan da wasu shekaru masu zuwa.

Shiga tsakanin Iran

Lallai Iran tana tsaka mai wuya a game da kulla alakar diflomasiyyar ta Saudiyya da Isra'ila. A wajenta, idan Amurka ta samu nasarar kulla alakar, ana yunkurin tilasta mata mika wuya ga Isra'ila ne.

Idan Saudiyya ta amince da Isra'ila, hakan zai sa ita ma Iran dole ta kara kaimi wajen karowa tare da karfafa alaka da kawayenta. Daga cikin wadanda za ta kara rikewa da kyau akwai kungiyoyin tada kayar baya irin su Hezbollah da ke Lebanon da Iraq, wadda ta dade tana yakin sunkuru da Isra'ila a madadin Iran.

Jami'an tsaro da 'yan kwanta-kwanta suna kokarin kashe gobara a wani gida da ke kusa da Ofishin Jakadancin Iran da ke Babban Birnin Damascus, na Syria wanda aka kai wa hari a ranar 2 ga Afrilun 2024. (AFP/Louai Beshara).

A wata alama da ke nuna cewa lallai Iran za ta kulla alaka da wadannan kungiyoyin, Shugaban Kasar Iran, Ebrahim Raisi ya yi gardadi a bara cewa dole duk wata kungiyar Musulunci a duniya ta kara kaimi wajen dage wajen adawa da makiyarta, musamman Iran.

Wani abun kuma shi ne, sulhunta alakar diflomasiyyar ta Saudiyya da Isra'ila za ta zama barazana a gare ta.

Bayan harin da aka kai hari a Ofishin Jakadancin Iran a Damascus a watan jiya, Saudiyya ta taimaka wajen kama daruruwan makamai da Iran ta aika Isra'ila.

Wannan lamarin, wanda Iran ta bayyana a matsayin kokarin kare 'yancinta. Idan har aka kulla alakar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Isra'ila har alakar ta fito fili, za ta iya kara tsananta zaman tankiya da ke tsakanin Saudiyya da Iran.

Idan har aka cimma yarjejeniyar kulla alakar, akwai yiwuwar karfin ikon Amurka a kan alakar Saudiyya da Isra'ila ya karu.

Yanzu haka Amurka na cikin masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro na Isra'ila, sannan ta hada kasar alaka da wasu kasashen Larabawa. Daga cikinsu akwai Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ba ta da alaka mai kyau da Iran, wanda hakan ke nufin kara dagula lissafin Iran na kara karfi a yankin na Larabawa.

Bayan haka, bukatun Isra'ila a bayyane suke. Shugabanninta na da burin amfani da kulla alakar diflomasiyya da Saudiyya ne domin samun damar kutsawa cikin yankin Larabawa.

Firaiminista Benjamin Netanyahu shi ma yana son kulla wannan alakar, amma ba ya so a kara yarjejeniyar daga wa Falasdinu kafa a ciki, wanda haka ne ra'ayin kasashe da dama da suke kawance da ita.

A bangaren kasashen duniya kuwa, Isra'ila ta yi amanna cewa gyara alakar diflomasiyya da Saudiyya zai taimaka mata wajen samun saukin kutsawa yankin na Larabawa, kamar su Kuwait da Oman. Lallai wannan alakar za ta kara jawo Isra'ila cikin harkokin tattalin arzikin yankin.

Don haka wannan yunkurin na Amurka na kulla alakar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Isra'ila zai yi tasiri sosai a yankin, wanda zai iya kawo tsaikon a kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Daga: TRT WORLD

Hannan Hussain babban mai sharhi ne a kan harkokin yau da kullum na duniya. Yana bincike a kan abubuwan da suka shafi tsaro da sulhu da alaka tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da Asia. Ya taba yin aikin a matsayin mai a Cibiyar Policy Research Institute (IPRI), sannan ya yi rubuce-rubuce a Mujallar Carnegie Endowment for International Peace da Mujallar Georgetown Journal of International Affairs, da Mujallar Express Tribune (wadda take aiki tare da Mujallar New York Times).

TRT World