Bayan an kwashe watanni biyar Isra'ila tana yaƙi a Gaza, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a karon farko ya amince a tsagaita wuta nan-take bayan Amurka ta janye daga kaɗa ƙuri'a.
Dukkan ƙasashe 14 mambobin kwamitin sun amince a tsagaita wuta "nan-take" a watan Ramadan yayin ƙuri'ar da suka kaɗa ranar Litinin, lamarin da sa aka kaure da tafi a zauren majalisar.
Ƙudurin ya yi buƙaci dukkan ɓangarorin su tsagaita wuta "nan-take a watan azumin Ramadan abin da ake fatan zai kai ga tsagaita wuta ta dindindin."
Kazalika ƙudurin ya yi kira a "gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharaɗi ba, tare da tabbatar da isar kayan agajin jinƙai na magunguna da sauransu" yankin Gaza.
Haka kuma ƙudurin ya buƙaci ɓangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar sakin mutanen da ke tsare a ƙarƙashin dokokin duniya.