Isra'ila ta yi ikirarin kai hare-hare ta sama kan mayakan Hamas da gine-ginensu ne amma yanayin da aka gani na wurin ya bayyana wani labari na daban. / Hoto: AA  

Fiye da kananan yara Falasdinawa 3,826 aka kashe a cikin kwanaki 27 da Isra'ila ta fara kai hare-hare a Zirin Gaza, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu.

An yi ta musu luguden wuta ta sama tare da tarwatsa su da rokoki da kuma rusa gine-gine waɗanda ɓaraguzansu suka yi sanadiyar danne mutanen a karkashin kasa, daga cikinsu akwai jarirai da 'yan yara da ɗalibai, da wadanda ke sha'awar zama 'yan jarida da yara maza da suka yi tsamanin za su tsira a cikin coci.

Kusan rabin jama'ar yankin da aka yi ƙawanya miliyan 2.3 'yan kasa da shekara 18 ne, kuma yara su ne kashi 40 cikin 100 na wadanda aka kashe kawo yanzu a yaƙin.

Wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya yi kan bayanan Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da aka fitar a makon jiya ya nuna cewa ya zuwa ranar 26 ga Oktoba, an kashe yara 2,001 'yan shekaru 12 zuwa kasa, ciki har da 615 wadanda ke tsakanin shekaru uku ko ƙasa da hakan.

"Lokacin da gidajen suka ruguje, sun fado kan kananan yara," in ji marubuci Adam al Madhoun a ranar Laraba yayin da yake jajantawa yanayin da 'yarsa Kenzi mai shekara hudu ke ciki.

Kenzi, wacce ta tsallake rijiya da baya a harin sama da Isra'ila ta kai, ta rasa hannunta ɗaya da illata ƙafarta ta hagu da kuma raunata kanta a Asibitin Kudus da ke tsakiyar birnin Deir al Balah a Gaza.

Isra'ila ta yi ikirarin kai hare-hare ta sama kan mayaƙan Hamas da gine-ginensu, amma yanayin hotunan da aka gani na harin ya nuna cewa maganarta ba gaskiya ba ce.

An kashe yara da dama a cikin makonni uku kacal a Gaza, adadin da ke zama mafi yawa idan aka kwatanta da tashe-tashen hankulan da duniya ta yi fama da su a shekaru ukun da suka gabata, a cewar kungiyar agaji ta Save the Children ta duniya.

Ga misali, kungiyar ta ce an kashe yara 2,985 a yankuna 12 da suka yi fama da tashe-tashen hankula a shekarar da ta gabata.

"Gaza ta zama makabarta ga dubban yara," in ji James Elder, kakakin hukumar UNICEF ta MDD da ke kula da lamuran da suka shafi yara.

"Mutane suna gudun mutuwa sai kuma su je su tarar da mutuwa''

Hotuna da bidiyon yara wadanda aka yi ƙoƙarin ciro su daga ɓaraguzan gine-gine da harin harsashi da bama-bamai Isra'ila a Gaza suka ruguza da yaran aka jera gawarwakinsu a kasan asibitoci masu datti sun zama ruwan dare gama duniya, lamarin da ke kara ruruta wutar zanga-zanga daga kasashen duniya.

Hotunan harin baya-bayan nan sun hada da na wani mai aikin ceto dauke da wata 'yar yarinya da aka lullube da farin ƙyalle da jini ya rina shi, da kuma wani uba da ke cikin yanayin alhini rungume da ɗansa da ya mutu a ƙirjinsa, sai wani yaro da ƙura da jini suka lulluɓe jikinsa yana birgima shi kadai a cikin wani gini.

"Ya zama babban laifi zama iyaye a Gaza," in ji Ahmed Modawikh, wani kafinta mai shekara 40 daga birnin Gaza wanda ya shiga cikin ƙuncin rayuwa sakamakon mutuwar 'yarsa 'yar shekara takwas a kwanaki biyar na wani yaƙin a watan Mayu.

Kazalika an kashe yaran Isra'ila, a lokacin harin ba-zata da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Isra'ila ta ce an kashe mata fiye da mutum 1,400, sannan ta ce aƙalla yara 30 suna daga cikin mutum kusan 240 da Hamas ta yi garkuwa da su.

Yayin da jiragen yakin Isra'ila suka yi ta luguden wuta a Zirin Gaza, yaran Falasdinawa da iyalansu ne suke cunkushe a wasu wurare ko matsugunai na MDD.

Duk da cewa Isra'ila ta bukaci Falasdinawan da su fice daga arewacin Gaza zuwa kudancin yankin, babu wani wajen da ake da tabbacin samun tsira daga hare-haren da take kai wa ta sama.

"Mutane suna gudun mutuwa sai kuma su je su tarar da mutuwar," a cewar Yasmine Jouda, wacce ta rasa ‘yan uwanta 68 a harin sama da aka kai ranar 22 ga watan Oktoba.

Harin ya yi sanadiyar tarwatsa wasu gine-gine masu hawa hudu a Deir al Balah, inda suka nemi mafaka daga arewacin Gaza.

Mutum daya tilo da ta tsira daga harin ita ce ‘yar ‘yar uwar Jouda mai shekara daya mai suna Milissa, wacce mahaifiyarta take naƙuda a lokacin da aka kai harin.

An samu gawarta a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe inda ake iya hango kawunan 'yan tagwayen jariranta da ke ƙoƙarin fitowa duniya.

"Me wannan 'yar jaririyar ta yi da ta cancanci a mayar da rayuwarta haka ba tare da danginta ba?" a cewar Jouda.

Falasdinawa sun bayyana karin adadin wadanda suka mutu a matsayin shaida ga ire-iren munanan hare-haren da Isra'ila ke kai musu.

Yaƙin ya raunata ƙananan yara Falasɗinawa sama da 7,000 tare da jefa da dama cikin mummunan yanayin da ya sauya rayuwarsu, a cewar likitoci.

Kafin a soma yaƙin, ‘yar ‘yar’uwar Jouda, Milissa, ta soma takun farko a rayuwarta. Yanzu ba za ta sake tafiya ba.

Likitoci sun ce harin da aka kai ta sama wanda ya yi sanadin kashe danginta ya karya mata ƙashin bayanta da ƙugunta tun daga ƙirjinta zuwa kasa.

Kusa da dakin da aka kwatar da ita kuma a tsakiyar asibitin Gaza mai cike da cunkoso, Kenzi ce 'yar shekara hudu ta farka tana kururuwa, tana tambayar me ya faru da hannunta na dama da aka guntule.

"Sai an yi aiki sosai wajen ba ta kulawar da za ta kai ta ga samun rabin rayuwa," in ji mahaifinta.

Hatta wadanda ba su ji wani rauni ba suna iya faɗawa cikin matsalar damuwa saboda irin ɓarnar da yaƙin ya janyo.

Ga yara 'yan shekaru 15 a Gaza, wannan shi ne yaƙinsu na biyar da suka taɓa gani tsakanin Isra'ila da Gaza da kuma ganin mutuwa ta ko ina.

Ga wasu kadan daga cikin yaran Falasdinawa kanana 3,648 da Isra’ila ta kashe.

Aseel Hassan 'yar shekara 13

Aseel Hassan ɗaliba ce mai ƙwazo, in ji mahaifinta, Hazem Bin Saeed. Ta ƙware sosai wajen rera waƙoƙin gargajiya.

A lokacin harin bama-baman Isra'ila, ta kan hada 'yan uwanta guri guda wajen rera musu shahararrun baituka daga wakokin Abu Al Tayyib al Mutanabbi, wani mawaƙi ɗan ƙasar Iraƙi, in ji mahaifinta.

“Lokacin da na tambaye ta abin da take so ta yi idan ta girma, sai ta ce, karatu,” in ji Bin Saeed mai shekaru 42. "Waki'o'i su ne abubuwan da Aseel ta tsira da su."

Wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a ranar 19 ga watan Oktoba ya ruguza gidansa mai hawa uku a Deir al Balah, inda ya kashe Aseel da ɗan uwanta mai shekara 14, mai suna Anas.

Majd Souri, ɗan shekara 7

Tashin bama-bamai sun firgita Majd, in ji mahaifinsa, Ramez Souri mai shekara 45.

Ya yi matuƙar kewar buga wasan ƙwallon kafa da abokansa na makaranta, sannan ya yi baƙin ciki kan cewa yaƙin ya soke ziyarar zuwa wajen danginsa Kiristoci da ke Nazarat, garin Isra’ila da ke da daɗaɗɗiyar al'adar cewa a can Annabi Isa (Jesus) ya girma.

"Baba ina za mu je?" Majd ya yi ta tambaya lokacin da aka tsananta kai hare-hare ta sama.

Iyalin na daya daga daidaikun masu kishin addinin Kirista a Gaza, a karshe suka sami amsar da suke nema na zuwa — Cocin Orthodox na St. Porphyrius na Greek a birnin Gaza.

Souri ya ce Majd ya samu nutsuwa a lokacin da suka koma cocin, inda mafi yawan iyalai Kiristoci suka fake, a tare suka addu'o'i da rera waƙoƙi.

A ranar 20 ga watan Oktoban ne, wasu gungun mayakan Isra'ila suka afkawa ciki wurin ibadar, inda suka kashe mutum 18, daga cikin wadanda suka mutu akwai Majd da 'yan uwansa, Julie mai shekaru 9 da kuma Soheil mai shekaru 15.

Kamar dai yadda ta saba, Isra’ila ta yi ikirarin cewa ta kai hari ne a wata cibiyar bayar da umarni na Hamas da ke kusa.

An same Majd a karkashin tarkacen ɓaraguzan da hannunsa kewaye da wuyan mahaifiyarsa, fuskarsa ta ƙone gaba ɗaya.

''Ya'yana kawai suna son zaman lafiya da kwanciyar hankali ne," in ji Souri, muryarsa cikin rawa yayin da ya fashe da kuka. "Damuwata ita ce su samu farin ciki."

Kenan da Neman al Sharif, 'yan watanni 18 da haihuwa

Karam al Sharif, ma'aikaci ne a hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu a hukumar MDD.

Da ƙyar ya iya yin magana ranar Laraba yayin da ya durƙusa kan gawarwakin 'ya'yansa kanana da aka lullube a asibiti. 'Ya'yansa mata sun tafi, Joud mai shekaru 5 da Tasnim mai shekaru 10.

Kazalika ya rasa ’ya’yansa tagwaye, ‘yan watanni 18 da haihuwa, Kenan da Neman.

Sharif ya yi kuka yayin da yake rungume da Kenan yana fadin cewa har yanzu ba a ga gawar Neman ba a karkashin baraguzan ginin bene mai hawa shida inda iyalan suka nemi mafaka a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza kafin Isra'ila ta kai masa hari.

"Ba su da sauran lokaci a nan," Sami Abu Sultan, ɗan'uwan Sharif, ya ce game da jarirai maza da suka mutu, kwana guda bayan ginin da Isra'ila ta tarwatsa.

Mahmoud Dahdouh, ɗan shekara 16

A ranar 25 ga Oktoba ne, tashar talabijin ta Aljazeera ta dauki wani yanayi mai ratsa zuƙata da shugaban ofishinta da ke Gaza, Wael Dahdouh ya gano cewa harin da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe matarsa da 'yarsa 'yar shekara shida da tattaɓa-kunnensa jariri da kuma ɗansa mai shekara 16, Mahmoud.

Yayin da kyamarorin daukar hoto na talabijin da ke asibitin suka mamaye shi, Dahdouh ya yi kuka a gawar kan matashin ɗansa yana cewa, "Kana son zama ɗan jarida."

Mahmoud ya kasance babban dalibi a makarantar sakandare ta Amurka da ke birnin Gaza, yana kuma da burin zama ɗan jarida na Turanci.

Ya kwashe lokacinsa yana koyon fasahar kyamarori tare da wallafa shirye-shiryen bayar da rahoto ta kafar YouTube, in ji Dahdouh.

Bidiyon da Mahmoud ya dauka kwanaki kafin rasuwarsa ya nuna motocin da suka ƙone, da hayaƙi mai duhu da ke tashi daga filaye da gidajen da suka ƙone.

Suna hira shi da 'yar uwarsa Kholoud wajen gabatar da abubuwan da suka faru.

"Wannan shi ne yaƙi mafi muni da tashin hankali da muka taɓa gani a Gaza," in ji Mahmoud.

A karshen daukar faifan bidiyon, yaran ​​sun zura wa kyamarar ido kai tsaye.

"Ku taimaka mana mu rayu kar a kashe my," suka bayyana a lokaci daya.

TRT World