Ƙasashen Turai na ci gaba da bai wa Isra'ila makamai yayin da take ƙara kai munanan hare-hare a Zirin Gaza sannan kuma ana zarginta da aikata laifin kisan ƙare-dangi.
Kamfanin dillacin labarai na Turkiyya Anadolu ya tattara wasu muhimman bayanai kan yadda kasashen Turai ke sayar wa Isra'ila makamai tun daga fara yaƙin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba na 2023.
A tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023 ƙasashen Faransa da Italiya da Jamus da kuma Amurka suna da kaso 81 cikin 100 na makaman da ake shigarwa yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar cibiyar nazari da bincike kan rikice-rikice da zaman lafiya a duniya Stockholm (SIPRI) da ke ƙasar Sweden.
Kudaden da Isra'ila ke kashewa na makamai ya ƙaru da kashi 24 cikin 100 zuwa dala biliyan 27.5 bayan hare-haren da ta kai a Gaza, lamarin da ya sa ta kasance ƙasa ta biyu a yawan kashe kudi kan makamai a Gabas ta Tsakiya.
Daga shekarar 2014 zuwa 2022, Ƙungiyar Tarayyar Turai EU ta ba da lasisin fitar da makaman da suka kai na kimanin dala biliyan 6.8 (€ 6.3 biliyan) zuwa Isra'ila.
Ana dai zargin wadannan makamai da sanadin mutuwar fararen hula fiye da 38,000 a Gaza, wadanda suka hada da mata 10,000 da ƙananan yara fiye da 15,000.
Ko da yake wasu kasashen Turai da suka hada da Belgium da Italiya da Netherlands da Sifaniya sun yanke shawarar dakatar da sayar da makamai ga Isra'ila, sai dai wasu rahotanni sun yi zargi cewa har yanzu akwai alamun ana ci gaba da cinikin makaman.
Manyan ƙasashen Turai da ke samar wa Isra'ila makamai
Jamus ta kasance ƙasa mafi girma a Turai da ke samar wa Isra'ila makamai, inda a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023 ta samar da kusan kashi 30 cikin 100 na yawan makaman da Isra'ila ke shiga da su ƙasarta.
A 2023, makaman da Jamus ta sayar wa Isra'ila ya ninka sau goma zuwa dala miliyan 353.8 (€326.5 miliyan) karin da aka samu bayan soma yakin ranar 7 ga watan Oktoba.
Yawancin makaman da Faransa ta ke fitarwa a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023 na zuwa ne ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya kai adadin kashi 34 cikin 100 na jimullar kayayyakin da take fitarwa.
Ƙasar ta yi fice wajen samar wa Isra'ila wasu fanni na makamai masu linzami, waɗanda aka fi sani da Iron Dome.
Duk da dokoƙin da suka haramta sayar da makamai ga masu take hakkin bil adama, Italiya ta sayar da makamai na dala miliyan 2.27 (€ 2.1) ga Isra'ila a cikin watannin karshe na shekarar 2023.
Ministan tsaron Italiya Guido Crosettoya ya yi ikirarin cewa ba a sake tura wasu makamai zuwa Isra'ila ba tun daga 7 ga Oktoba, sai dai an samu rahotanni da ke nuna cewa kamfanoni irin su Leonardo sun ci gaba da siyar da makaman.
Izinin fitar da kayayyakin Italiya zuwa Isra'ila na shekarar 2019 zuwa 2022 da suka hada da jiragen yaki da kananan makamai da manyan bindigogi da jiragen sama da harsasai, sun kai na dala miliyan 123.5 (€114 miliyan).
Tun daga shekarar 2015 Birtaniya ta ba da izinin fitar da makamai na sama da dalar Amurka miliyan 576 ga Isra'ila.
Kazalika, kashi 15 cikin 100 na kayayyakin da ake amfani da su wajen kera jiragen yakin F-35 da Isra'ila ta sayo tun a shekarar 2016, kamfanonin Birtaniyya ne suka samar, a cewar wani rahoto da ƙungiyar agaji ta Action on Armed Violence da ke birnin Landan ta fitar.
Ba a samu wani rahoto daga ƙasar Sifaniya na siyar da makamai ga Isra'ila ba tun daga ranar 7 ga Oktoban bara, amma bayanai a watan Nuwamban 2023 sun nuna cewa an yi musayar albarusai na dala miliyan 106 (€ 987,000).
Tsakanin 2014 zuwa 2022, Sifaniya ta ba da izinin fitar da makamai da suka kai na dala miliyan 107 (€ 99 miliyan), cikin har da harsashi da motocin soji.