Nijeriya ta kwashe 'yan kasarta sama da mutum 300 daga Isra'ila. Hoto: Gwamnan Legas/X

Kasashe da dama a fadin duniya sun soma kwashe ‘ya'yansu daga Isra'ila, yayin da wasu kasashen ke shirin yin hakan a cikin kwanaki masu zuwa sakamakon rikicin da ke faruwa tsakaninta da mayakan Hamas a Gaza.

Ga wasu bayanai game da shirye-shirye da kuma inda aka kwana kan aikin kwashe mutanen, kamar yadda bayanan da majiyoyin hukumomi suka nuna.

Ukraine

Kasar Ukraine ta shirya tashin jirgi na farko daga birnin Tel Aviv a ranar Asabar, ana kuma sa ran na biyu zai tashi ranar Lahadi, a cewar jakadan Kyiv a Isra'ila Yevgen Korniychuk a ranar Laraba.

Sakamakon dakatar da zirga- zirgar jiragen sama zuwa Ukraine da aka yi saboda rikicin kasar da Rasha, a yanzu haka ana sa ran jiragen za su sauka a kasashen da ke makwabtaka da Ukraine ne kamar Moldova da Romaniya da Slovakiya da kuma Poland, kamar yadda jakadan ya shaida wa wani gidan talabijin na kasar.

'Yan Ukraine dubu daya ne suka nemi a kwashe su. "Akwai babbar matsala ga 'yan kasarmu da ke Gaza," kuma adadinsu ya kai 300, in ji jakadan.

Hukumomi sun hada ''jimillar sunayen mutane kusan 160 da za a kwashe daga Zirin Gaza -- kuma adadin mutanen na dada karuwa --daga nan za a wuce zuwa Masar ta Rafah, sannan zuwa kasa ta uku,'' in ji shi.

Canada

Canada ta aika da jirgin sama na sojoji guda biyu wadanda za su iya ''jigilar kwaso mutanenta" zuwa gida "a cikin kwanaki masu zuwa", in ji ministar harkokin waje kasar Melanie Joly.

Fiye da ƴan Canada 4,200 ne suka yi rajista da babban ofishin jakadancin Ottawa da ke Isra'ila sannan wasu mutum 470 a Falasdinu.

Girka

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Girka ta ce an riga an kwashe da 'yan kasarta kusan 90 daga Isra'ila.

Sannan an shirya dawowar wani jirgi zuwa Girka a safiyar ranar Alhamis agogon Girka.

Argentina

A ranar Talata ne, kasar Argentina da ke yankin Latin Amurka mai yawan al'umma Yahudawa ta fara kwashe sama da 'yan kasarta 1,200 daga Isra'ila.

Jiragen soji n sama guda uku a rana zai dauki 'yan Argentina 1,246 da suka nemi a kwashe su zuwa Rome babban birnin Italiya, in ji ministan tsaro Jorge Taiana.

Daga nan ne kamfanin jirgin sama na Aerolineas Argentinas na gwamnati zai yi jigilar su zuwa Buenos Aires.

Brazil

Gwamnatin Brazil na shirin hada wasu jiragen sama akalla guda shida a wani yunkuri na maido da duk wani dan kasarta da ke son barin Isra'ila da Falasdinu cikin gaggawa.

A cewar gwamnatin kimanin 'yan Brazil 14,000 ne ke zaune a Isra'ila, 6,000 kuma a yankunan Falasdinawa.

Jirgin farko dauke da 'yan kasar Brazil mutum 211 ya dawo kasar kafin wayewar ranar Laraba, ana sa ran dawowar jirgi na biyu ranar Alhamis.

Wasu 'yan kasar sun riga sun tashi a jiragen kasuwanci, in ji gwamnati.

Nijeriya

Nijeriya ta kwaso 'yan kasarta fiye da 300 zuwa gida bayan da suka tsere zuwa kasar Jordan daga Isra'ila, inda suka kai ziyara ta aikin ibada na Kiristanci, a cewar Gwamnatin jihar Legas.

Bayan barkewar rikicin ne hukumar aikin ibada ta Kiristanci a Nijeriya tare da taimakon kugiyar mabiya addinin Kiristanci na kasar suka shirya tafiyarsu zuwa kasar Jordan sannan aka yi musu hayar jirgi zuwa Legas.

Switzerland

Kamfanin jiragen sama na Swiss International Air Lines ya dawo da ‘yan kasar Switzerland 220 zuwa gida, sannan an shirya dawowar jirgi na biyu na musamman da zai kwaso mutm 215 a ranar Laraba.

Kazalika an shirya dawowar jirgi na uku mai adadin kujeru 215 a ranar Alhamis, wanda ake sa ran zai sauka a Tel Aviv da rana.

Kimanin 'yan kasar Switzerland 28,000 da iyalansu ne aka yi wa rajista a hukumance a don zama a Isra'ila da yankunan Falasdinu.

Sifaniya

A cikin daren ranar Talata zuwa Laraba Kasar Sifaniya ta shirya dawowar wani jirgi daga Tel Aviv dauke da mutane 209, daga ciki akwai 'yan kasar 185 sai kuma sauran daga kasashen Turai da Latin Amurka.

Bayan nan Jirgin na biyu ya tasi daga Tel Aviv da rana dauke da fasinjoji 220, daga ciki akwai 'yan kasar Sifaniya 149.

Koriya ta Kudu

Wani jirgin dauke da 'yan kasar Koriya ta Kudu 192 ya taso daga Tel Aviv inda ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Incheon da ke kusa da birnin Seoul da sanyin safiyar ranar Laraba, a cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Za a kwashe wasu mutane 30 'yan Koriya ta Kudu nan gaba a wannan makon ta jiragen kasuwanci, in ji ma'aikatar tare da karin kan cewa wasu mutune 27 da su kawo ziyarar addini Isra'ila za su bi kan hanya ta makwabciyar kasar Jordan zuwa kasarsu.

Faransa

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta sanar da cewa an tura wani jirgin Air France na musamman zuwa birnin Tel Aviv a ranar Alhamis domin kwashe duk wani dan Faransa da ya makale.

Jamus

Jamus ta ce tana aiki tare da kamfanin jirgin sama na Lufthansa don shirya "jirage na musamman" a ranakun Alhamis da Juma'a da za su maido da 'yan kasarta.

Kusan 'yan Jamus mutum 4,500" ne suka yi rajistar sunayensu a cikin jerin wadanda ke neman taimakon komawa gida, in ji wata majiyar ma'aikatar harkokin waje kasar

Iceland

Gwamnatin Iceland ta sanar da cewa za ta aike da jirgin da zai maido da 'yan kasarta kusan mutum 120 da suka makale a Isra'ila.

Norway

Ita ma kasar Norway ta shirya wani jirgin da yammacin ranar Laraba da zai kwaso mata ‘yan kasarta da suka makale a Isra’ila da kuma yankunan Falasdinawa. Akwai kusan yan kasar Norway mutum 500 a yankin.

Portugal

A safiyar Laraba ne kasar Portugal ta dawo da ‘yan kasarta mutum 152 da kuma wasu Turawa 14, a cikin wani jirgin saman sojin kasar .

Australiya

Gwamnatin kasar Australiya ta sanar da cewa ta dawo da mutane 98 a yammacin ranar Laraba, daga ciki akwai yan kasar 83 da kuma wasu mutune 15 da suka hada da yan' Isra'ila da Jamusawa da Sipaniya da Hungarian da Amurka da kuma Dutch.

TRT Afrika