Za su yi da na sanin yin hakan," kamar yadda aka ambato Khamenei yana faɗa a ranar Talata. Hoto: AFP

Jagoran addini na Iran Ali Khamenei ya ce ƙasashen da ke neman shiryawa da Isra'ila 'za su yi saki reshe kama ganye ne", a cewar kafar yada labaran kasar.

"Matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan wannan batun shi ne duk ƙasashen da ke son shirya wa da Isra'ila za su yi saki reshe kama ganye. Za su yi da na sanin yin hakan," kamar yadda aka ambato Khamenei yana faɗa a ranar Talata.

Akwai yiwuwar wata yarjejeniyar sasantawa tsakanin Isra'ila da Saudiyya da Amurka ta kaddamar za ta fara aiki nan da shekara mai zuwa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Isra'ila ya faɗa a watan da ya wuce, bayan da ƙasashen uku suka fara nuna alamun samun ci gaba a batun sasantawar mai sarƙaƙiya.

Saudiyya, inda a can ne wurare mafiya tsarki na Musulunci Makkah da Madina suke, ba ta taɓa ɗaukar Isra'ila a matsayin ƙawa ba kuma ta daɗe ɗa faɗar cewa ba za ta yi hakan ba in har ba a warware rikicin Isra'ila da Falasɗinu ba, da kuma bai wa ƴan gudun hijirar Falaɗinu mafaka.

Sai dai kuma, gwamnatin Shugaba Joe Biden na ƙoƙarin ganin an cimma wata yarjejeniya mai tarihi da za ta iya sauya tsarin dangantakar Gabas ta Tsakiya ta hanyar sasanta ƙasashen biyu da suka kasance manyan abokan hulɗar Amurkar ko don ma bai wa Iran haushi - wani salo na cimma wani ƙudurin hulɗarta da ƙasashen waje da zai gyara wa Shugaba Biden hanya a takarar da zai sake tsayawa a zaɓen 2024.

Wani ministan Israi'la ya isa Saudiyya a ranar Litinin don halartar wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda shi ne ministan Isra'ila na biyu da ya ziyarci Saudiyyan a ƙasa da mako guda.

Ministan Sadarwa Shlomo Karhi ya je birnin Riyadh don ganawa da wata hukuma ta MDD da ke da alhakin kula da sashen akwatin gidan waya na ƙasa da ƙasa.

Riyadh tana neman samun taimakon Amurka ne kan shirin nukiliya a madadin wannan yarjejeniyar sasantawar da Amurkan ke son a cimma, don samun damar inganta fannin makamashin yuraniyom ɗinta.

Falasɗinawa sun yi gargaɗin cewa dole ne a saka muradunsu a kowace irin yarjejeniya da za a yi, kuma har yanzu ba a san irin alakawuran da za ta iya ɗauka kan hakan ba.

TRT World