Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024
1328 GMT –– An sake jikkata sojojin Isra'ila biyar a Gaza
Sojojin Isra'ila 5 sun jikkata sakamakon arangamar da aka yi a Zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Alkaluman da sojojin suka fitar na nuni da cewa, an kashe wasu sojoji 798 tare da jikkata wasu 5,370 tun bayan fara yakin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
1230 GMT –– Yawan mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun kai 43,922 yayin da take ci gaba da muzguna wa yankin
Akalla karin Falasdinawa 76 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,922, in ji ma’aikatar lafiya a yankin.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 103,898 sun suka samu raunuka a harin da ake ci gaba da kai wa.
Ma'aikatar ta ce: "Mamayar Isra'ila ta yi kisan gilla ga iyalai hudu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 76 da jikkata 158."
"Mutane da yawa har yanzu suna makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da kungiyoyin agaji suka kasa kai musu hari," in ji ta.
0842 GMT –– Sabbin hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 26 a kudancin Lebanon
Aƙalla mutum 26 ne suka mutu sannan gommai suka jikkata bayan da Isra'ila ya ƙddamar da wasu sabbin hare-haren sama a kudancin Lebanin, in ji kafar yaɗa labarai ta ƙasar.
Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-haren sama 10 a birnin Nabatieh, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas tare da jikata wasu da dama, in ji kamfanin dillancin labaran NNA.
Sannan an kashe wasu ma'aikatan lafiya shida a wani harin sama da aka kai Hukumar Lafiya ta Musuluncin a garin Arab Salim.
Kazalika wani mutum ɗayan ya sake rasa ransa a harin da aka kai gundumar Bent Jbeil, a cewar NNA.
Jiragen yaƙin Isra'ila sun kuma ƙaddamar da hare-hare da dama a yankunan da ke kusa da Tyre, lamarin da ya kashe mutum 11 tare da jikkata 48, in ji kamfanin dillancin labaran.
0549 GMT –– Harin da Isra'ila ta kai a yankin Mawasi na Gaza ya kashe mutun 4 'yan gida ɗaya
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa WAFA ya ruwaito cewa Isra'ila ta kashe mutane da dama, ciki har da yara, a harin bama-bamai da ta kai da sanyin safiya a kudancin Gaza.
Majiyoyi daga asibiti sun ce dakarun Isra'ila sun kashe mutum huɗu 'yan gida ɗaya –– wani mutum da matarsa da 'ya'yansa. 'Yarsu ta tsallake rijiya da baya amma ta samu raunuka masu muni, sakamakon luguden wutar da sojojin Isra'ila suka yi a wani tanti da 'yan gudun hijira suke samun mafaka a yankin Al Mawasi da ke yammacin Khan Younis.
Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a yankin Al Mawasi na Gazaduk da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana shi a matsayin "tudun-mun-tsira."
Mazauna yankin sun ce Isra'ila ta sha kai musu hari babu ƙaƙƙautawa.
Ƙarin labarai👇
0633 GMT –– 'Wani abin fashewa' ya faɗa kudancin Jordan ba tare da jikkata kowa ba: Rundunar sojin Jordan
Rundunar sojin Jordan ta ce "wani abin fashewa" ya faɗa a yain da ke kan iyaka na lardin Aqaba da ke kudancin Isra'ila.
Wata sanarwa ta ambato majiyoyin soji suna cewa babu wanda ya jikkata sakamakon faɗuwar abin.
Ta ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa wurin da lamarin ya faru.
Sai dai sanarwar ba ta faɗi sunan abin da ya faɗa a yankin ba, ko kuma daga inda aka harba shi. Birnin Aqaba yana daura da birnin Eilat na kudancin Isra'ila.