Laraba, 22 ga Janairu, 2025
2224 GMT –– Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare a birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla tara da jikkata aƙalla mutum 40, in ji jami'in kiwon lafiyar Falasɗinu, a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta ƙulla da Hamas ta shiga kwana na huɗu a Gaza.
A Tel Aviv, an jikkata mutum huɗu a wani hari da aka kai musu da wuƙa ko da yake jami'an tsaro sun kashe mutumin da ya kai harin, a cewar 'yan sandan Isra'ila.
Hukumomi sun ce mutumin da ya kai harin "ɗan ƙasar waje" kuma yana da shekaru 28 suna masu cewa harin na ta'addanci ne.
2100 GMT — Motocin agaji aƙalla 2,400 sun shiga Gaza
Kimanin motocin agaji 900 sun shiga Gaza a yayin da wani babban jami'i na MDD ya ce kawo yanzu babu wani ƙalubale da ya shafi karya doka.
Hakan na nufin a jumlace motocin agaji 2,400 sun shiga yankin wanda aka mamaye.
A watanni 15 da Isra'ila ta kwashe tana yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza, MDD ta bayyana shigar da kayan agaji yankin a matsayin babban ƙaluale — inda dakarun Isra'ila suke hana ma'aikatanta gudanar da ayyukansu sannan gungun 'yan Isra'ila suna sace kayan na agaji.
Muhannad Hadi, wani babban jami'i na MDD a Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ya ce a kwana uku da suka wuce ba a samu satar kayan agaji da yawa ba, "ba kamar a baya ba."
2000 GMT — An gano gawawwaki da suka zagwanye a ƙarƙarshin ɓuraguzan gidaje
Falasɗinawa da dama a birnin Rafah na kudancin Gaza sun koma gidajensu sai dai sun yi matuƙar kaɗuwa da ganin yadda aka wawashe komai a shaguna da gidajen nasu.
Manal Selim, wata mata mai 'ya'ya shida, da ke sana'ar gyaran gashi kuma tana da kantin sayar da kayan aure na mata, ta ce an sace komai daga shaguna da gidanta.
"Mun yi tsammanin za mu samu wani abu, ko kuma mu samu wurin zama," in ji ta. . "Ɓarnar ta girgiza mu."
A nasa ɓangaren, wani ma'aikacin agaji ya ce sun gano gawawaki da dama a ƙarƙashin ɓuraguzan gine-gine da Isra'ila ta ruguza.
"A cikin kwana biyu mun gano gawwaki 120 da suka zagwanye. Sun yi matuƙar zagwanyewa ta yadda ƙasusuwa ne kawai suka rage," a cewar Haitham Hams a hira da kamfanin dillancin labaran Associated Press.