Wasu gungun Yahudawa ‘yan kama wuri zauna da haɗin gwiwar sojojin Isra’ila sun kai samame tsohon birnin Hebron, da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan. / Hoto: AA      

0420 GMT — Yahudawa 'yan kama wuri zauna tare da haɗin gwiwar sojojin Isra'ila sun afka ƙauyuka da birane da dama a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a ranar Asabar da dare, wanda hakan ya sa suka yi fito-na-fito da Falasɗinawa.

Gidan talabijin na Falasɗinu ya bayar da rahoton cewa an jikkata mutum guda a lokacin samamen da 'yan kama wuri zauna suka kai waɗanda sojojin na Isra'ila ke ba su kariya a ƙauyen Umm Safa da ke arewacin Ramallah.

Sai dai rahoton bai yi bayani kan irin raunin da aka ji wa mutumin ba.

Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya yi nuni da cewa, wasu da dama daga cikin 'yan kama wuri zaunansun afka Umm Safa, inda suke harba harsasai a kan gidajen mutane.

0504 GMT — Aƙalla Falasɗinawa hudu aka kashe a harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya ce jiragen yaki sun yi ruwan bama-bamai a yankin da ke kusa da mahadar Abu Sarrar da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

Falasdinawa uku ne suka mutu a harin, yayin da motocin sojin Isra'ila kuma suka yi luguden wuta mai tsanani kan sansanin.

Sojojin sun kuma kai hari kan wani gida na iyalan Suweidan a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin Gaza.

TRT Afrika da abokan hulda