Talata, 21 ga Janairu, 2025
0913 GMT —Trump ne tunzura Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna - Hukumar Falasɗinawa
Hukumar Falasɗinawa ta ce matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na janye takunkuman da aka sanya wa Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan shi ne yake tunzura su wajen cin zarafin Falasɗinawa.
"Cire takunkuman da aka sanya wa 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi zai ƙarfafa musu gwiwa wajen aikata ƙarin laifuka kan mutanenmu", a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinawa ta fitar.
Ma'aikatar ta jawo hankali game da hari na baya bayan nan da 'yan kama-wuri-zauna suka kai wa Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan wanda ya jikkaya mutum 21.
0706 GMT — 'Yan kama-wuri-zauna na Isra'ila sun kai hari a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, sun jikkata Falasɗinawa 21
Falasɗinawa fiye da 21 sun jikkata yayin da Isra'ilawa 'yan kama-wuri-zauna suka kai hari a garuruwa biyu na Falasɗinawa kusa da birnin Qalqilya a arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Ƙungiyar bayar da agaji ta Palestinian Red Crescent Society ta ce tawagarta ta likitoci ta bayar da magunguna ga mutanen da suka jikkata sakamakon harin na 'yan kama-wuri-zauna a garuruwan Jinsafut da Al-Funduq.
Mutanen sun kukkuje sakamakon dukan da 'yan kama-wuri-zauna suka yi musu, sannan dakarun Isra'ila suka fesa musu tiyagas, a cewar ƙungiyar bayar da agajin.
'Yan kama-wuri-zauna sun kai harin ne a yayin da ake ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wadda Qatar, Masar da Amurka suka shiga tsakani wajen ƙulla ta ranar Lahadin da ta gabata.
0112 GMT —Trump ya nuna shakku kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shakkunsa game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a yayin da aka tambaye shi kan ko yana da ƙwarin gwiwa game da yiwuwar aiwatar da dukka matakai uku na yarjejeniyar.
A yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishin shugaban ƙasa bayan sanya hannu kan dokokin shugaban ƙasa, Trump ya ce yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya ya yi kama da "wani babban wuri da aka rusa" kuma ya kamata a sake gina shi a wani tsari na daban.
Ƙarin labarai 👇
0107 GMT — Trump ya soke takunkuman da aka sanya wa 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Shugaban Amurka Donald Trump ya soke takunkuman da tsohuwar gwamnatin Biden ta ƙaƙaba wa Isra'ilawa 'yan kama-wuri-zauna bisa musguna wa Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda sabon shafin intanet na Fadar White House ya bayyana.
Shafin ya ce Trump ya soke Dokar Shugaban Ƙasa mai lamba 14115 wadda aka amince da ita ranar 1 ga watan Fabrairun 2024, wacce kuma ta amince a sanya takunkumai kan "mutanen da ke yin tarnaƙi game da zaman lafiya da tsaron Gaɓar Yammacin Kogin Jordan."