Illegal settlers set fire to crops, trees in occupied West Bank

1500 GMT — Yahudawa 'yan kama waje zauna sun cinna wa gonaki da shuka wuta a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da aka mamaye

Yahudawa 'yan kama waje zauna na Isra'ila sun kona filayen noma na Falasdinawa da ke kusa da birnin Nablus a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, inda suka mayar da amfanin gonakin hatsi da itatuwan zaitun zuwa toka.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, da gangan wasu gungun Yahudawa 'yan kama waje zauna na Isra'ila sun ƙona gonaki a garin Bayt Furik da ke gabashin birnin Nablus.

Wutar ta ƙone wani yanki mai yawa na shukar hatsi da itatuwan zaitun, duk da kokarin da Falasdinawa suka yi na kashe ta, in ji shaidun.

A gefe guda kuma, matsugunan Yahudawa 'yan kama waje zauna na Isra'ila a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan sun lalata amfanin gonakin Falasdinawa ta hanyar kiwon tumakinsu a cikin gonakin, kamar yadda majiyar kasar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Wani lamari da ya faru a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan ya faru lokacin da wasu matsugunan Yahudawa 'yan kama waje zauna na Isra'ila suka lalata amfanin gona a kasar Falasdinu yayin da suke kiwon tumakinsu, in ji majiyoyin cikin gida.

0415 GMT — An kwashe sojojin Isra'ila 200 daga sansanin soji da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan saboda tashin gobara a kusa da su

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar a yau Juma'a cewa ta kwashe wasu sojoji 200 daga wani sansanin soji da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye sakamakon wata gobara da ta tashi a kusa da wajen.

Shafin yada labarai na Isra'ila Ynet ya bayar da rahoton cewa, rundunar sojin ta kwashe dakarun daga wani sansani da ke kusa da kudancin Kfar Etzion yayin da gobara ta tashi a wani budadden wuri da ke kusa da sansanin.

Sai dai rundunar sojin ba ta faɗi abin da ya tayar da gobarar ba.

Shafin intanet ɗin ya ƙara da cewa an aika tawagar 'yan kwana-kwana 20 da jirage shida don ƙoƙarin shawo kan gobarar.

Kfar Etzion wani matsugunin Isra'ila ne da aka gina a kasar Falasdinu a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.

A karkashin dokokin kasa da kasa, ana daukar duk matsugunan Yahudawa a yankunan da aka mamaye.

1105 GMT — Ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya 'damu matuka' kan tashin hankalin da ke ta'aazara tsakanin Lebanon da Isra'ila

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya damu matuka dangane da rikicin da ke faruwa tsakanin Lebanon da Isra'ila.

"Mun damu matuka game da lamarin - inda aka kashe daruruwan mutane, dubbai suka jikkata, wasu dubban kuma suka rasa muhallansu, tare da karin sa'insa masu sanya damuwa," in ji mai magana da yawun Ravina Shamdasan yayin amsa tambayar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yi masa.

"Muna jaddada bukatar kwantar da tarzoma da kuma dakatar da tashin hankali," in ji Shamdasan.

Ta buƙaci da a gudanar da cikakken bincike kan duk wani lamari da ya shafi kisan fararen hula, tana mai cewa "hakan na da muhimmanci."

Ta kara da cewa ofishin kare hakkin bil'adama ya samu rahotanni masu "saka matukar damuwa" na yara da ma'aikatan jinya da 'yan jarida a cikin wadanda aka kashe.

1024 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kutsawa cikin kudanci da arewacin Gaza

Sojojin Isra'ila sun sake kutsawa cikin yankuna biyu na arewaci da kudancin Gaza, kuma jami'an kiwon lafiyar Falasdinu sun ce harin tankokin yaki a Rafah ya kashe akalla mutum 11.

Sojojin Isra'ila sun kara kutsawa cikin kudanci da arewacin Gaza / Hoto: AFP

Mazauna yankin da kafafen yada labarai na cikin gida sun ce tankokin yaki sun kara yin yamma zuwa unguwar Shakoush da ke Rafah, lamarin da ya tilasta wa dubban mutanen da suka rasa matsugunansu barin sansaninsu, suka nufi arewa zuwa Khan Younis da ke kusa.

Wani mazaunin yankin, wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce wasu manyan katafiloli a yankin Shakoush na tara yashi domin tankunan yaƙin Isra'ila su samu tsayawa a baya.

Ya ƙara da cewa, “Wasu iyalai suna zaune a yankin da aka kai farmakin, kuma a yanzu dakarun mamaya sun yi wa wajen ƙawanya.

"Halin da ake ciki yana da matukar hadari kuma iyalai da yawa suna tafiya zuwa Khan Younis, har ma daga yankin Mawasi, saboda al'amura sun kasance marasa aminci a gare su," in ji mutumin, wanda ya koma arewa cikin dare.

A gefe guda kuma, sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai sabon farmaki a unguwar Shujaiya da ke arewacin Gaza, inda tankokin yaƙi suka kutsa wajen a ranar Alhamis.

TRT Afrika da abokan hulda