Litinin, 20 ga Janairu, 2025
0828 GMT — Jami'an jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya sun ce manyan motoci fiye da 630 ɗauke da kayayyakin agaji sun shiga Gaza da aka yi wa ƙawanya, a wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tsakanin isra'ila da Hamas.
A wani saƙo da aka wallafa a shafin X, ƙaramin sakatare na ayyukan jinƙai na MDD, Tom Fletcher ya ce fiye da manyan motocin kaya 630 ne suka shiga Gaza a ranar Lahadi, inda aƙalla 300 daga cikinsu suka shigar da kayan agaji cikin arewa.
Fletcher ya rubuta cewa, "Ba za mu ɓata lokaci ba."
2335 GMT — Isra'ila ta saki Falasɗinawa fursunoni 90
Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta ce ta kammala sakin Falasɗinawa fursunoni 90, a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta soma aiki ranar Lahadi.
"An saki dukkan fursunoni daga gidan yarin Ofer da kurkukun Birnin Ƙudus", in ji wata sanara da hukumar ta fitar kafin ƙarfe 1:30 na dare.
Wata babbar motar ɗaukar kaya, ɗauke da gomman fursunonin, dukkansu mata da ƙananan yara, ta fita daga kurkukun Ofer da ke wajen birnin Ramallah na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Dukkan waɗanda aka saka mata da ƙananan yara ne, a cewar wani jadawali a Hukumar Kula da Harkokin Gudanarwar Falasɗinawa.
0244 GMT — Gazawar Isra'ila ta cim ma burinta ne ta tilasta mata amincewa a tsagaita wuta: Hamas
Gazawar Isra'ila ta cim ma burinta ne ta tilasta mata sassauta ra'ayinta a teburin sulhu, a cewar Mohammad Nazzal, wani babban jami'i a fannin siyasa na ƙungiyar Hamas.
"Burin Isra'ila shi ne ta kuɓutar da mutanenta da aka yi garkuwa da su, ta rusa masu gwagwarmaya — musamman Hamas — sannan ta mamaye ɗaukacin Gaza. Babu ɗaya daga cikin muradunta da ya biya," in ji Nazzal a keɓantacciyar tattaunawa da Anadolu Agency.
"Sun kasa yin amfani da ƙarfin soji don kuɓutar da mutanensu da aka yi garkuwa da su don haka sai suka sassauta matsayinsu a lokacin tattaunawa. A halin da ake ciki, babu yadda za a kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su idan ba ta hanyar sulhu ba," a cewarsa.
2352 GMT — Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun yi murnar dawowar 'yan'uwansu
Dandazon mutane sun taru a garin Beitunia da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda suka riƙa murnar sakin 'yan'uwansu daga gidajen yarin Isra'ila.