Hayaki na tashi kuma wuta na ci daga makarantar Salah al-Din, mafaka ga Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, sakamakon harin da Isra'ila ta kai a unguwar er-Rimal da ke birnin Gaza. /Hoto: AA

Juma'a, 15 ga Nuwamban 2024

0124 GMT — Wani jigo a kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya jaddada cewa a shirye suke don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a matsayin wani bangare na musayar fursunoni "mai tsanani".

Basem Naim, wani likitan Falasdinu, ɗan siyasa kuma jigo a ofishin siyasa na Hamas, ya ce "yarjejeniya mai kyau da aka fayyace ta ƙarshe" ita ce ranar 2 ga Yuli.

"An tattauna dalla-dalla, kuma ina tsammanin muna kusa da tsagaita wuta… wanda zai iya kawo karshen wannan yakin, ya kawo tsagaita wuta na dindindin da janyewa baki daya da kuma musayar fursunoni," in ji shi a wata hira da Sky News.

Naim ya ce "Abin takaici, (Firaministan Isra'ila Benjamin) Netanyahu ya gwammace ya bi ta wata hanya" ya kuma tunatar da cewa "Isra'ila ta yi kisan kiyashi akalla biyu zuwa uku" a Khan Younis da kuma birnin Gaza bayan haka.

Dangane da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na Hamas Ismail Haniyeh a watan Yuli, ya ce tun bayan hakan, ba su sami "wata sahihiyar magana ba."

Karin bayani 👇

0003 GMT — Bam da aka harba daga Lebanon ya raunata sojojin Isra'ila 2

Sojojin Isra'ila biyu sun jikkata sakamakon fashewar wani jirgin mara matuki da aka harba daga kudancin Lebanon zuwa arewacin Isra'ila, a cewar rundunar.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta bayar da rahoton cewa, jirgin mara matuki ya fado kuma ya fashe a sansanin Eliakim da ke kudancin Haifa bayan da sojojin tsaron saman Isra'ila suka fatattake su na kusan mintuna 40.

TRT World