Falasɗinawa da ke  Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun yi ta murnar sakin 'yan'uwansu daga gidajen yarin Isra'ila. / Hoto: AFP

Litinin, 20 ga Janairu, 2025

2335 GMT — Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta ce ta kammala sakin Falasɗinawa fursunoni 90, a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta soma aiki ranar Lahadi.

"An saki dukkan fursunoni daga gidan yarin Ofer da kurkukun Birnin Ƙudus", in ji wata sanara da hukumar ta fitar kafin ƙarfe 1:30 na dare.

Wata babbar motar ɗaukar kaya, ɗauke da gomman fursunonin, dukkansu mata da ƙananan yara, ta fita daga kurkukun Ofer da ke wajen birnin Ramallah na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Dukkan waɗanda aka saka mata da ƙananan yara ne, a cewar wani jadawali a Hukumar Kula da Harkokin Gudanarwar Falasɗinawa.

0244 GMT — Gazawar Isra'ila ta cim ma burinta ne ta tilasta mata amincewa a tsagaita wuta: Hamas

Gazawar Isra'ila ta cim ma burinta ne ta tilasta mata sassauta ra'ayinta a teburin sulhu, a cewar Mohammad Nazzal, wani babban jami'i a fannin siyasa na ƙungiyar Hamas.

"Burin Isra'ila shi ne ta kuɓutar da mutanenta da aka yi garkuwa da su, ta rusa masu gwagwarmaya — musamman Hamas — sannan ta mamaye ɗaukacin Gaza. Babu ɗaya daga cikin muradunta da ya biya," in ji Nazzal a keɓantacciyar tattaunawa da Anadolu Agency.

"Sun kasa yin amfani da ƙarfin soji don kuɓutar da mutanensu da aka yi garkuwa da su don haka sai suka sassauta matsayinsu a lokacin tattaunawa. A halin da ake ciki, babu yadda za a kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su idan ba ta hanyar sulhu ba," a cewarsa.

2352 GMT — Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun yi murnar dawowar 'yan'uwansu

Dandazon mutane sun taru a garin Beitunia da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda suka riƙa murnar sakin 'yan'uwansu daga gidajen yarin Isra'ila.

TRT World